Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m

Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya gabatar da kansa a gaban kwamitin tantance yan takarar sanata a ranar Asabar don a tantance shi
  • Hakan na zuwa ne duk da cewar Oshiomhole ya ayyana kudirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa harma ya siya fom din naira miliyan 100 na APC
  • A takaice hakan ya nuna tsohon gwamnan na Edo ya mallaki fom biyu na shugaban kasa da sanata don shirin ko ta kwana

Abuja An tantance tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, domin takarar kujerar sanata a karkashin jam’iyyar mai mulki.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Oshiomhole ya bayyana a gaban kwamitin tantancewar duk da cewar ya biya naira miliyan 100 na fom din shugaban kasa tare da kaddamar da kamfen dinsa na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m
Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m Hoto: @aoshiomhole
Asali: Twitter

An tattaro cewa tsohon gwamnan na jihar Edo ya isa wajen tantancewar da ke Fraiser Suite, Abuja, da misalin karfe 8:12 na dare.

Da farko Oshiomhole ya ayyana kudirinsa na takarar sanata mai wakiltan Edo ta arewa. Sai dai kuma daga bisani ya bayyana kudirinsa na shugaban kasa a wani babban taro a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanzu dai a bayyane yake cewa tsohon shugaban kungiyar kwadago na kasar ya mallaki fom biyu na shugaban kasa da na sanata.

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

A wani labarin, tsohon sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya, Sanata Basheer Garba Mohammed (Lado), ya bayyana cewa ba za a iya yi masa makarkashiya don lalata kudirinsa na komawa majalisar dattawa ba a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, Sanata Lado ya nesanta kansa daga rahoton kwanan nan kan wani furuci da aka alakanta da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Daily Trust ta rahoto.

Sanata Lado ya rantse cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai sanya shi yankan fom din takara ba, yana mai cewa duk labarin kanzon kurege ne kuma kage ne don jan hankalin jama’a da kuma yunkurin bata sunansa da na Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel