Ka yage 'yan jari hujja daga jikinka - Farfesa Sagay ya shawarci Buhari
- Farfesa Itse Sagay, shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan yaki da cin hanci, ya shawarci shugaba Buhari da ya yage 'yan jari hujja daga jikinsa
- Sagay ya ce 'yan jari hujjar sun mamaye harkokin mulki a fadar shugaban kasa
- Farfesa ya ki yarda ya furta sunan mutanen da ya kira da cewar su ne 'yan jari hujjar a fadar shugaban kasa
Shugaban kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin zakulo hanyoyin dakile cin hanci da kuma hukunta wadanda aka samu da laifin cin hanci, Farfesa Itse Sagay, ya shawarci Buhari da ya gaggauta yage 'yan jari hujjar dake kewaye da shi.
Farfesa Sagay ya yi wannan kira ne a jiya yayin ganawar sa da manema labarai bayan ya gabatar da jawabi a wurin bikin yaye daliban jami'ar kimiyya ta Minna dake jihar Naija.
Duk da bai yarda ya furta sunan kowa daga cikin mutanen da ya kira 'yan jari hujjar ba, Farfesa Sagay, ya ce sun mamaye harkokin mulki a fadar shugaban kasa. Sannan ya kara da cewa, lokaci ya yi da shugaba Buhari zai yakice su tunda basa rike da kowanne mukami a gwamnatance.
DUBA WANNAN: PDP ta kwarmata wata yaudara da ta zargi jam'iyyar APC na kullawa
Da yake amsa tambaya a kan badakalar mayar da Maina bakin aiki, Farfesa Sagay, ya ce akwai bukatar a zakulo dukkan masu hannu cikin yanke shawarar mayar da Maina tare da hukunta su domi ya zama darasi ga duk masu mayar da kokarin gwamnati a yaki da cin hanci baya.
A jawabin da ya gabatar ga daliban da aka yaye, Farfesa Sagay, ya bukace su da su goya wa Buhari da Osinbajo baya domin mutane ne masu kima da kishin kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng