2023: Bayan Fita Daga APC, Adamu Garba Ya Bayyana Sabuwar Jam'iyyar Da Ya Koma,Ya Ba Matasa Haƙuri

2023: Bayan Fita Daga APC, Adamu Garba Ya Bayyana Sabuwar Jam'iyyar Da Ya Koma,Ya Ba Matasa Haƙuri

  • Cikin kasa da awanni 24 bayan Adamu Garba ya bar jam’iyyar APC saboda tsadar fom din takara, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar YPP
  • Dan takarar shugaban kasar, ya bai wa magoya bayansa hakuri dangane da matakin da ya dauka inda ya ce APC ta rasa nagartarta, ta koma kasuwanci da kudin jama’a
  • Idan ba a manta ba, a ranar 18 ga watan Afirilu Adamu Garba ta bayyana cewa ze tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar APC

Ko kwana daya ba a yi ba, bayan dan takarar shugaban kasa, Adamu Garba ya bayyana batun sauya shekarsa daga jam’iyyar APC saboda tsadar fom din takara, ya koma jam’iyyar Young Peoples Party, YPP.

Ya fara ne da bai wa masoyansa hakuri dangane da barin APC din da ya yi inda ya ce jam’iyyar ta mayar da zaben fidda gwaninta hanyar kasuwanci da dukiyar jama’a hakan ya sa ya sauya sheka, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Adamu Garba Ya Ba Matasa Haƙuri, Ya Bayyana Sabuwar Jam'iyyar Da Ya Koma
Adamu Garba Ya Bayyana Sabuwar Jam'iyyar Da Ya Koma, Ya Ba Matasa Haƙuri. Hoto: @adamugarba
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, Adamu Garba ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a ranar 18 ga watan Afirilu.

Adamu Garba ya ce shi mai kishin Najeriya ne

Sai dai a takardar da ya saki a ranar Alhamis a Twitter, ya ce ba zai juri yin abinda ya san zai kawo cikas ga tsaron kasar nan ba, ya ce yana sa ran abubuwa za su gyaru.

Ya kara da cewa:

“Ni mai kishin Najeriya ne kuma ba zan yi wani abu da na san zai kawo matsala ga tsaro da kuma zaman lafiyar kasar nan ba.
“Ina ji a jikina cewa abubuwa za su gyaru komai rintsi. A gaskiya na yi wasu kura-kurai a wasu bangarori, saboda abubuwa da dama ba su gyaru ba, sai ma kara lalacewa da su ka yi.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

“Ina da buri mai yawa da tunanin komai zai sauya, amma da alamu APC ba ta da shirin gyara ko kuma burin ci gaban matasa.”

Ya fadi dalilinsa na komawa YPP

Ya bayyana cewa APC tana ta tatsar jama’a ta hanyar sayar musu da fom mai tsada kuma su na gani mutane su na mutuwa wasu kuma su na ta tserewa daga kasar maimakon su tsaya su ci bakar wahala.

A cewarsa, shugabanninmu ba su damu ba saboda a ganinsu ma’adanai su na kara auki yayin da mutane su ke mutuwa wasu kuma su na guduwa daga kasar nan.

Ya yi alkawarin dagewa da kuma zage damtse wurin yin aiki don ya riga ya gane kura-kuransa. Kuma a shirye ya ke da ya dage wurin samar da sabuwar Najeriya. Amma hakan ba zai yiwu ba da tsofaffin shugabanni.

A cewarsa wannan ne dalilinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar YPP.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

2023: NNPP Ta Ce Kwankwaso Ne Zai Zama Shugaban Ƙasa, Ta Haɗa Kai Da Ƙungiyoyi 1000

A wani labarin, jam’iyyar NNPP ta hada kai da Kungiyoyi masu zaman kansu, NGOs fiye da 1,000 da Kungiyoyi masu kare hakkin bil’adama da za su mara wa jam’iyyar baya a zaben 2023, The Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana yakininta akan goyon bayan da su ke ta samu, kuma sun yarda da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne zai zama sabon shugaban kasar Najeriya.

Jami’in hadin kan jam’iyyar NNPP, Bashir Mohammed Abacha ya bayyana hakan yayin taron jam’iyyar da kuma Kungiyoyi masu zaman kansu da su ka yi rijista da jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel