'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

  • Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nisanta kansa daga wallafar Twitter wacce ya yi alawadai da kisan Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari
  • A jiya ne aka samu bayanai dangane da kisan dalibar, wacce kirista ce ‘yar aji biyu a kwalejin bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW
  • Sai dai bayan Atiku ya yi suka akan kisan nata, musulmai sun yi caa akansa su na cewa ba za su zabe shi ba, hakan ya sa ya dawo ya ce ba ya da masaniya akan wallafar

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Sakon Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba
'Batanci: Atiku ya nesanta kansa daga wallafar suka akan kone dalibar Sokoto. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Ya nesanta kansa daga wallafar ne bayan musulmai sun yi barazanar kin zabensa

Sai dai bayan wasu musulmai na arewa sun fara barazanar cewa ba za su zabe shi ba idan PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takara, Atiku ya janye furucinsa.

Daga bisani Atiku ya goge wallafar da ya yi da kuma barazanar da aka dinga yi masa karkashin wallafar.

Sannan ya yi wata wallafa da harshen Hausa wacce ya nisanta kansa daga wallafar ta farko. Kuma a cewarsa duk wallafar da aka yi a shafukan sada zumuntarsa wacce ba ta zo da A. A. ba, ba shi ya rubuta ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

"Cikin wannan dare na samu bayanin cewa anyi wani rubutu da babu amincewa da umarni na. Da wannan nake amfani na sanar da cewa duk wani rubutu da babu alamar AA ba daga wajena bane. Allah ya kiyaye - AA", in ji shi.

‘Yan takara da dama ba su yi suka akan kisan Deborah ba

Kamar yadda ya ce:

“Da yamman nan na ga wata wallafa wacce aka yi ba da izininna ba. Ina amfani da wannan damar domin shaida wa kowa cewa duk wallafar da aka yi babu A. A. ba tawa ba ce. Ubangiji ya kare mu.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yanke shawarar goge wallafar ne bayan yadda aka yi caa akan shi, yanzu haka yana daya daga cikin wadanda ake ta magana a Twitter.

The Punch ta ruwaito cewa ‘yan takara da dama sun ki yin ala-wadai akan kisan Deborah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel