2023: NNPP Ta Ce Kwankwaso Ne Zai Zama Shugaban Ƙasa, Ta Haɗa Kai Da Ƙungiyoyi 1000

2023: NNPP Ta Ce Kwankwaso Ne Zai Zama Shugaban Ƙasa, Ta Haɗa Kai Da Ƙungiyoyi 1000

  • Jam’iyyar NNPP a ranar Alhamis ta jero sunayen kungiyoyi masu zaman kansu fiye da 1,000 da Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da za su mara wa jam’iyyar baya a zaben 2023
  • Jam’iyyar ta nuna yakininta dangane da goyon bayan da za su samu wanda su ke kyautata zaton tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya zama shugaban kasar Najeriya
  • Jami’in kawo hadin kai da NNPP din, Bashir Mohammed Abacha, ya bayyana hakan yayin taron da jam’iyyar ta yi da kungiyoyin wadanda su ka yi rijista da jam’iyyar

A ranar Alhamis, jam’iyyar NNPP ta hada kai da Kungiyoyi masu zaman kansu, NGOs fiye da 1,000 da Kungiyoyi masu kare hakkin bil’adama da za su mara wa jam’iyyar baya a zaben 2023, The Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana yakininta akan goyon bayan da su ke ta samu, kuma sun yarda da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne zai zama sabon shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

2023: NNPP Ta Ce Kwankwaso Ne Zai Zama Shugaban Ƙasa, Ta Haɗa Kai Da Ƙungiyoyi 1000
NNPP Ta Hada Kai Da Kungiyoyi 1000, Ta Ce Kwankwaso Zai Zama Shugaban Kasa. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’in hadin kan jam’iyyar NNPP, Bashir Mohammed Abacha ya bayyana hakan yayin taron jam’iyyar da kuma Kungiyoyi masu zaman kansu da su ka yi rijista da jam’iyyar.

A cewarsa, an yi taron ne musamman don sanin kalubale da kuma hanyoyin da za a tabbatar da burin kungiyoyin ya tabbata.

Ya ce a wurin taron akwai kungiyoyi 50 da su ka yi wa rijista

The Punch ta ruwaito yadda Abacha ya ce:

“Ba wai mun gama yin rijistar Kungiyoyi 50 kawai ba ne. Muna da kungiyoyi da dama kuma su na karkashin ofishina. Mun fara taro iri-iri kuma yanzu haka akwai NGOs guda 50 a wannan taron. Mun yi rijistar NGOs din.
“Wannan shi ne dalilin hakan, kuma idan za ka yi zabe ya kamata ka tattaro naka mutanen. Kungiyoyin daga fadin kasar nan, jihohi da kananun hukumomi su ke. Idan ka yi rijista da hukumar yi wa kamfanoni rijista, akwai damar da za a iya samu daga mutane daga gundumomi da kuma tarayya.

Kara karanta wannan

Sanatan Kebbi ta tsakiya: Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC

“Shiyasa mu ka hada kai da su don tabbatar da mun gina kungiya mai kyau da jama’a na kwarai.”

Ya ce mutane su na ta guduwa daga APC da PDP su na komawa NNPP

Yayin bayani akan yiwuwar Kwankwaso ya lashe zaben 2023, Abacha ya ce babu dan siyasar da ya ke da karfin kayar da Kwankwaso.

A cewarsa a manta da batun manyan sunayen ‘yan siyasar da ake ji, Kwankwaso babban dan siyasa ne. Ya taba rike kujerar gwamna, minista da kuma sanata. Duk da dai ya fadi zabe amma ya kara komawa a matsayin gwamna kuma babban dan siyasa ne.

Ya bayyana yadda mutane su ke ta shiga jam’iyyar NNPP yayin da su ke ta guduwa daga PDP da APC. Ya ce mutane da dama su na ta ganin kokari da kuma ayyukan da ya yi a baya hakan ya sa su ke goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel