‘Yan Majalisar Kano da Kwamishinan Ganduje, sun bi Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

‘Yan Majalisar Kano da Kwamishinan Ganduje, sun bi Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

  • Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi za ta karbi wasu ‘yan siyasa da suka fice daga tafiyar APC
  • ‘Yan Majalisar dokoki uku ne su ka yi watsi da jam’iyyar APC, duk za su sauya-sheka zuwa NNPP
  • Nura M. Dankadai zai sauya-sheka ‘yan kwanaki kadan bayan ya yi murabus a Gwamnatin Ganduje

Kano - Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu ya nuna cewa jam’iyyar NNPP ta sake yin kamu a jihar Kano, inda ta samu karin mabiya a makon nan.

Jam’iyyar hamayyar ta NNPP ta samu karin ‘yan majalisar dokoki uku da suka sauya-sheka daga APC kamar yadda suka sanar a wasikar da suka fitar.

A mabanbantan takardu da suka aikawa shugaban majalisar Kano a ranar 5 ga watan Mayun 2022, sun sanar da cewa komawarsu jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Darektan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Kano, Uba Abdullahi ya kawo sunayen wadanda suka fice daga jam'iyyar mai rinjaye.

Su wanene su ka bar APC?

Akwai Hon Abdullahi Iliyasu Yaryasa mai wakiltar mazabar Tudun Wada. Sai kuma Hon. Muhd Bello Butu Butu mai wakiltar mutanen Tofa da Rimin Gado.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na uku a jerin shi ne Hon. Kabiru Yusuf Ismail, ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Madobi.

Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Hakan na nufin an samu masu sauya-shekan daga kowane yanki na Kano. Yayasa ya fito ne daga kudancin jihar, Butu Butu kuma yana Arewacin jihar Kano.

Kabiru Yusuf Ismail shi ne yake daga garin Madobi a shiyyar Kano ta tsakiya. Madobi ce mahaifar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Malam Uba Abdullahi ya ce majalisa ta yi wadanda suka fice daga jam’iyyar APC fatan alheri. Jaridar Premium Times ta kawo irin wannan rahoto dazu.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Nura M. Dankadai zai koma NNPP?

Baya ga haka, Legit.ng Hausa ta samu labari Nura M. Dankadai ya bar APC. A watan jiya ne Dankadai ya ajiye kujerar Kwamishinan kasafi da tsare-tsare.

Hon. Dankadai ya ce ya fice daga jam’iyya mai mulki ne saboda yadda aka maida mutanen Tudun Wada/Doguwa saniyar ware. Ana tunanin yana shirin bin NNPP.

'Yan NNPP sun haura 10 a Majalisa

A makon jiya an karanta rahoto cewa Isyaku Ali Danja, Umar Musa Gama, Aminu Sa’adu Ungogo, da Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa sun fice daga PDP.

Sauran ‘yan majalisar da suka koma NNPP su ne Tukur Muhammad, Mu’azzam El-Yakub, Garba Shehu, Abubakar Uba Galadima da Mudassir Ibrahim Zawaciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng