Siyasar Kano: Wasu ‘Yan Majalisa 9 sun bi su Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

Siyasar Kano: Wasu ‘Yan Majalisa 9 sun bi su Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

  • Wasu ‘yan majalisar dokoki sun yi watsi da jam’iyyar PDP da ba ta ba su nasara a zaben da ya wuce
  • Ana rade-radin cewa akalla mutane tara da ke majalisar jihar Kano ne su ka tsallaka zuwa NNPP
  • Rt. Hon. Isyaku Ali Danja mai wakiltar Gezawa ya na cikin zugar ‘yan majalisar da suka sauya-sheka

Kano - Legit.ng Hausa ta samu labari cewa wasu daga cikin ‘yan majalisan dokoki na jihar Kano sun sauya-sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Rahotannin da mu ke samu shi ne ‘yan majalisar sun koma jam’iyyar hamayyar nan ta NNPP.

Wata sanarwa da ake ikirarin ta fito daga Darektan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Kano, Uba Abdullahi ya tabbatar da haka.

An karbi takardun sauya-shekan da ‘yan majalisar dokokin su ka gabatar ga shugaban majalisa na Kano, inda aka sanar da shi game da ficewarsu daga PDP.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Daga cikin dalilan da masu sauya-shekar suka bada shi ne sabanin cikin gidan da ya dabaibaye jam’iyyar hamayyar ta sa dole suka tsallaka zuwa NNPP.

A halin da ake ciki PDP ta na fama da rigimar shugabanci tsakanin Shehu Wada Sagagi da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar da suka huro wuta cewa sai an tsige shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Magoyan Jam’iyyar NNPP
'Yan Kwankwasiyya Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Ban san da maganar ba – Shugaban PDP

A ranar Juma’ar nan Legit.ng Hausa ta tuntubi Alhaji Shehu Wada Sagagi a game da wannan jita-jita, inda ya tabbatar mana da cewa bai san da labarin ba.

Sagagi ya tabbatar mana da cewa ‘yan majalisar sun nemi su yi zama da shi, amma ba su samu damar haduwa ba har aka fara yada labarin ficewar ta su.

Shugaban PDP na jihar Kano ya yi alkawarin zai tuntube mu da zarar ya bibiyi halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Kano da Kwamishinan Ganduje, za su bi Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

‘Yan majalisar da suka sauya-sheka:

1. Rt Hon. Isyaku Ali Danja (Gezawa)

2. Hon. Umar Musa Gama (Nassarawa)

3. Hon Aminu Sa'adu Ungogo (Ungogo)

4. Hon Lawan Hussain Chediyar 'Yan Gurasa (Dala)

5. Hon. Tukur Muhd (Fagge)

6. Hon.Mu'azzam El-Yakub (Dawakin Kudu)

7. Hon. Garba Shehu Fammar (Kibiya)

8. Hon. Abubakar Uba Galadima (Bebeji)

9. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki (Kumbotso)

'Yan majalisa sun aika takardun barin PDP

Legit.ng Hausa ta ga takardar Hon. Lawal Husseini, ‘dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala da yake bada sanarwar komawarsa jam'iyyar NNPP.

Shi ma Hon. Umar Musa Gama ya aikawa shugaban PDP na mazabarsa ta Gama a Nasarawa takarda, yana sanar da shi cewa ya fice daga jam’iyyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel