Shigar Jonathan APC Zai Zama Ɗaya Cikin Abubuwa Mafi Ban Mamaki a Wannan Ƙarnin, In Ji Umahi

Shigar Jonathan APC Zai Zama Ɗaya Cikin Abubuwa Mafi Ban Mamaki a Wannan Ƙarnin, In Ji Umahi

  • Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi ya ce idan har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya koma APC labarin zai shiga littafin tarihi na duniya
  • Hadin kan kungiyoyin arewa sun siya wa tsohon shugaban kasar fom din takara karkashin inuwa jam’iyyar APC a ranar Litinin, inda su ka bukaci ya tsaya takara
  • Bayan nan ne Jonathan ya ki amincewa da kungiyar kana ya nisanta kansa daga duk wasu ayyukan da mambobin kungiyar su ke yi

Ebonyi - Dave Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya ce idan har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya koma jam’iyyar APC, labarin zai shiga littafin tarihin duniya, The Cable ta rahoto.

A ranar Litinin, hadakar kungiyoyin arewa su ka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takara karkashin jam’iyyar APC, inda su ka bukaci ya tsaya takara.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Umahi: Abu Ma Fi Ban Mamakin da Zai Faru a Wannan Ƙarnin Shi Ne Jonathan Ya Koma APC
Abu Ma Fi Ban Mamakin da Zai Faru a Wannan Ƙarnin Shi Ne Jonathan Ya Koma APC, Umahi. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ganin hakan ne Jonathan ya nuna ba ya da masaniya da kungiyar sannan ya nisanta kansa daga duk ayyukan mambobin kungiyar.

Yayin da Umahi ya ke jawabi a gidan gwamnatin jihar ranar Talata, Ya ce an siya fom din ne musamman don a tozarta Jonathan kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya ce Jonathan uba ne a wurinsa

The Cable ta bayyana yadda gwamnan ya je gidan gwamnatin don ya gabatar da takardar godiya daga shugabannin kudu maso gabas ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin kwanakin nan, shugaban kasa ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu Jihar Ebonyi.

Yayin jawabi dangane da halin da Jonathan ya ke, Umahi ya ce abu mai wahala ne jam’iyya mai mulki ta yi wa tsohon shugaba kasar kamfen.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

“Jonathan uba ne a wurina kuma Ubangiji ya yi amfani da shi da matarsa inda su ka mayar da ni gwamna. Don haka duk wanda ya kyautata min, ina girmama shi har abada, tare da matarsa da su taimaka min wurin cika buri na.
“Ba na manta wadanda su ka taimaka mana amma batun komawarsa APC, ba ni da abubuwa da yawa da zan ce amma akwai rubuce-rubuce da dama da na gani. Idan har ya shiga jam’iyyar to wannan zai zama abin al’ajabin da ya faru a wannan karnin.”

Ya ce an siya fom din ne don tozarta Jonathan

Ya ci gaba da cewa:

“Dalilina kuwa shi ne, idan har ka ga yadda ‘yan APC su ke kamfen, yanzu kuma su ka bukaci Jonathan ya tsaya takara, ban san wanne alkawarin kamfen da labarai da za mu dinga ba ‘yan Najeriya ba.”

Ya ci gaba da cewa ya tabbatar Jonathan bai san da batun siyan fom dun ba kuma an siya ne duk don a tozarta shi.

Kara karanta wannan

Akpabio: 'Gaskiyar' Buhari Ta Sa Na Shiga Jam'iyyar APC

Ya bayyana cewa a abubuwan da ya karanta, ya gano cewa Jonathan ya yi gaggawar nesanta kansa daga batun. Kuma da ya amince da wannan labarin sai ya shiga littafin tarihin duniya.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel