Akpabio: 'Gaskiyar' Buhari Ta Sa Na Shiga Jam'iyyar APC
- Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya ce ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC a 2018 ne saboda gaskiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin tafiyar da ayyuka a Najeriya
- Akpabio ya kara da cewa ya koma APC ne don ya taimaka wa Buhari musamman bayan ganin akwai wasu na hannun damansa da ke yunkurin kyale shugaban kasar
- Sai dai ministan bai bayyana ko su wanene na hannun daman shugaban kasar da su ka yi yunkurin cin amanarshi ko share shi ba
Godswill Akpabio, Ministan harkokin Neja Delta ya ce abinda ya sanya shi barin jam’iyyar PDP don ya koma APC a shekarar 2018 shi ne ganin gaskiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayin tafiyar da harkokin kasar nan.
Sannan Akpabio ya ce ya koma APC ne don tallafa wa Buhari bayan ganin amintattunsa su na yunkurin kyale shi, Premium Times ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana:
“Akwai dalilan da su ka sanya ni komawa jam’iyyar. Na farko shi ne na ga gaskiyar Shugaban Kasa. Na ga kuma kokarinsa a lokacin ina majalisar tarayya.”
Akpabio ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi wanda ta wallafa a YouTube ranar 5 ga watan Mayu.
Ya ce kowa ya cire son zuciya ya mayar da hankali kan ci gaban kasa
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya ci gaba da cewa:
“Na ga wadanda su ka yi kokarin ganin ya hau karagar mulki su na yunkurin cin amanarsa hakan ya sa nace a’a, wannan ba zai faru ba saboda ya kamata ka duba Najeriya.
“Bai dace ka ci gaba da kallon kanka kadai ba. Ko da kana murna ko ba ka yi da gwamnati, ya kamata ka dubi Najeriya, hakan ya sa na koma jam’iyyar don in taimaka masa ta hanyar ciyar da kasar nan gaba.”
Ministan bai bayyana ko su wanene su ke yunkurin cin amanar shugaban kasar ba.
Bayan Akpabio ya koma PDP, an samu rahoton yadda ya ce a shekarar 2015, zuciyarsa ta Buhari ce ba shugaban kasa Goodluck Jonathan ba, duk da dai daga baya ya zabi Jonathan a zaben shugaban kasa.
Akpabio ya rike kujerar gwamnan Jihar Akwa Ibom na shekaru 8 karkashin jam’iyyar PDP.
Daga baya aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a 2015, amma daga bisani ya yi murabus daga kujerarsa a matsayin shugaban marasa rinjaye a 2018 inda ya koma APC.
Sai dai bai samu nasarar komawa majalisar dattawan ba a 2019.
Ya ce APC ba ta da bambanci da PDP
Akpabio bai dade da bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa ba a 2023 inda ya ce APC ba ta da bambanci da PDP.
Ya kara da cewa:
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba
“Kila dai daga suna ne, maganar gaskiya. A gareni kuwa, babu bambanci tsakanin jam’iyya mai mulki da ta adawa.
“Jam’iyyu kamar kasuwa ne. Mutane su na shiga su fita. Wadanda su ka fara PDP yanzu su ne a APC. Na san mutane da dama da su ka bar APC a 2019, bayan mako daya su wasu su ka tsaya takarar shugaban kasa, sanata ko gwamna.”
Akpabio ya ce zai fi mayar da hankali kan harkar tsaron Najeriya da kuma bunkasa tattalin arziki tare da rabuwar kawuna idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng