Ta kanmu mu ke, ba ta kashe N100m ba: Miyetti Makiyaya sun musanta sayen fom ga Jonathan

Ta kanmu mu ke, ba ta kashe N100m ba: Miyetti Makiyaya sun musanta sayen fom ga Jonathan

  • Kungiyar Fulani makiyaya ta MACBAN ta musanta cece-kucen da ake na cewa Fulani sun sayi fom ga tsohon shugaba Jonathan
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da labari ya karade kasa cewa wasu makiyaya da Fulani 'yan Arewa sun ware kudin sun sayi fom ga JonathaKungiyar ta yi bayani, ta ce a yanzu dai ita ma ta kanta take, don haka maganar sayen fom din N100m bai ma taso ba

Birnin Tarayya, Abuja - Kungiyar Fulani ta Miyetti-Allah MACBAN, ta ce ba ta sayi fom din tsayawa takara ga wani dan takara da zai fafata a zaben 2023 mai zuwa ba, inji rahoton Daily Nigerian.

Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin ne rahotanni suka ce kungiyar Fulani makiyaya ta sayawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, duk da cewa ya ki amincewa da hakan.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Martanin Miyetti Allah ga sayen fom din Jonathan
Rudani: Miyetti-Allah ta musanta sayen fom din takarar shugaban kasa ga Jonathan | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren kungiyar ta MACBAN na kasa, Baba Ngelzarma, a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, ya nisanta kansa da kungiyar ga wannan ci gaba.

Mista Ngelzarma ya yi kira ga ’yan jarida da su ba da lokacinsu don fahimtar bambancin kungiyoyin Fulani daban-daban, su guji jawo MACBAN cikin hauragiyar siyasa, kamar yadda The Nation ma ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kan mu muke, ba ta sayen fom ga dan takara ba

A cewarsa:

“An jawo hankalin hedikwatar MACBAN ta kasa kan wani labari mai cike da rudani wanda a cikinsa ake cewa mun sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben 2023.
“Muna so mu bayyana cewa MACBAN bata saya ba kuma ba za ta siya kowane fom na kowane dan takara da zai fafata a zabe ba.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

“A matsayinmu na kungiya muna da bukatu masu yawa na kudi don taimaka wa mambobinmu da ake tashin su da kashe su a wasu sassan kasar nan.
“MACBAN ba ta ganin wata riba a cikin irin wannan hauragiya da ba ta da wani amfani ga miliyoyin mambobinmu da ke cikin halin kaka-nika-yi cikin bakin talauci sakamakon barnar ‘yan fashi da masu satar shanu.”

Sakataren ya ce kungiyar ta MACBAN ta yi imanin cewa ya kamata a bar siyasa a hannun ‘yan siyasa, yana mai cewa:

“Ba mu ga wata fa'ida ta tallafa wa kowane dan siyasa ba a lokacin da rikicin da mambobinmu ke fuskanta a fadin kasar nan ke ta'azzara."

A cewarsa, MACBAN, idan bukatar hakan ta taso, za ta goyi bayan dan takarar da ya nuna jajircewa wajen kawo karshen wahalhalun da ‘ya’yan kungiyar ke ciki bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar da dukkanin jam’iyyun siyasa ke yi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

Ya kara da cewa:

“Muna sa ran ganin manufofin ‘yan takara daban-daban da kuma inda ya dace da mambobinmu domin tantance wadanda za su marawa baya.”

Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m

A wani labarin kuma, wata kungiyar arewacin Najeriya da ta hada da Fulani makiyaya da al'ummar Almajirai, a ranar Litinin a Abuja ta ce ta shirya bai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan kuri'u miliyan 14 a zaben shekara mai zuwa.

Kugiyoyin sun sanar da cewa sun siyar da shanunsu masu yawa domin tattara N100 miliyan na siyan masa fom din takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Idan za a tuna, a ranar Juma'a, 22 ga watan Afirilun 2022, wata kungiya ta tsinkayi ofishin tsohon shugaban kasan da ke Abuja inda ta bukace sa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel