Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m

Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m

  • Kungiyar Fulanin Najeriya da almajirai ta sha alwashin kawowa Goodluck Jonathan kuri'u miliyan 14 a zabe mai zuwa
  • A ranar Litinin ne kungiyar ta lale kudi har N100 miliyan inda ta siya wa Jonathan fom din takara karkashin jam'iyyar APC
  • Shugaban kungiyar, Ibrahim Abdullahi, ya ce sun siyar da shanu masu yawa kafin hada N100m ganin tallafawa Fulani da almajirai da yayi a baya

FCT, Abuja - Wata kungiyar arewacin Najeriya da ta hada da Fulani makiyaya da al'ummar Almajirai, a ranar Litinin a Abuja ta ce ta shirya bai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan kuri'u miliyan 14 a zaben shekara mai zuwa.

Kugiyoyin sun sanar da cewa sun siyar da shanunsu masu yawa domin tattara N100 miliyan na siyan masa fom din takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m
Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Idan za a tuna, a ranar Juma'a, 22 ga watan Afirilun 2022, wata kungiya ta tsinkayi ofishin tsohon shugaban kasan da ke Abuja inda ta bukace sa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Tun a watan Afirilu, sauran kungiyoyi sun nuna rashin jin dadinsu ga shugabancin jam'iyyar APC inda suka ja kunnen jam'iyya da kada ta kuskura ta tsayar da Jonathan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan siyan fom din, shugaban kungiyar, Ibrahim Abdullahi, ya ce sun yanke shawarar ne ganin irin tarihi mai kyau da Jonathan ya bari na tallafawa Almajirai da al'ummar Fulani.

Kamar yadda yace, "Mun shirya ba siyan fom kadai ba ga Goodluck Jonathan, ina son tabbatar muku da cewa al'ummar mu, fulani makiyaya na da karfin ikon kuri'u miliyan tara da kuma mashawarta da za su iya kawo kuri'u miliyan biyar, kusan miliyan 14 kenan. Muna kira ga sauran 'yan Najeriya da su ba mu a kalla kuri'u miliyan biyu, ka ga mun kai kenan."

Kara karanta wannan

2023: Moghalu Ya Lale N25m Ya Biya Kuɗin Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyarsa

2023: Abin Da Jonathan Ya Ce Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takara a APC

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom ɗin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progresives Congress, APC, da wata kungiyar magoya bayansa daga arewa suka siya masa, rahoton Daily Trust.

Jaridar The Cable ta ce Ikechukwu Eze, mashawarcin Jonathan a bangaren watsa labarai, ya bayyana hakan awannin bayan labarin cewa an siya masa fom ɗin yana mai cewa ba a nemi izinin tsohon shugaban kasar ba kuma ya dauki shi a matsayin 'cin mutunci'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel