Alkawari kaya: Abubuwa 5 da Tinubu ya ce zai yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Alkawari kaya: Abubuwa 5 da Tinubu ya ce zai yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

  • Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina inda ya gana da Gwamna Aminu Masari a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu
  • Dan takarar na shugaban kasa a APC ya yi wa wakilai da masu ruwa da tsaki alkawarin cewa zai tura isassun kayan aiki don magance matsalar 'yan bindiga idan ya gaji Buhari
  • Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce zai mayar da hankali ne wajen ci gaba a fannin ilimi da tattalin arziki

Katsina – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan Legas, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ya yi tsokaci kan abin da wasu ka iya cewa manufofinsa ne na siyasa a shirin zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar na APC na kasa ya bayyana wasu manufofi guda biyar da zai mayar da hankali a kai idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Tinubu ya yi alkawarin cire 'yan Najeriya daga talauci
Alkawarin siyasa: Abubuwa 5 da Tinubu ya ce zai yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari | Hoto: channelstv.com
Asali: Depositphotos

A yayin da yake magana da wakilan jam’iyyar a ranar Litinin a Katsina, Tinubu ya bayyana cewa yana da duk abin da ya kamata na tafiyar da mulkin kasar nan.

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samo, ya bayyana cewa ya mallaki dukkan wasu abubuwan da ake bukata don a gan shi a matsayin wanda zai iya zama shugaban kasar Najeriya saboda dimbin ilimi da gogewarsa da kuma irin nasarorin da ya samu a harkokin siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubuwan da Tinubu zai yi idan ya gaji Buhari

A ci gaba da haka, Tinubu ya sha alwashin cimma abubuwa kamar haka idan aka ba shi damar mulkar Najeriya:

  1. Ka hada kan 'yan Najeriya da kara musu fata ba tare da la'akari da kabila ko addini ba
  2. Kirkirar sabbin dabaru da kaddamar da isassun kayan aiki don yakar 'yan bindiga da sauran laifuka masu alaka idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa
  3. Mai da hankali kan ci gaban tattalin arziki
  4. Mai da hankali kan Ilimi
  5. Bunkasa ababen more rayuwa don farfado da Najeriya daga bacci

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

A kalamansa, cewa ya yi:

“Na zo ne domin in hada Najeriya ba don in raba ta ba; Na zo ne in kawo muku fata, wadata, farin ciki, aiki, da kwanciyar hankali. Ko da harsuna ka iya bambanta, ’yan’uwantaka zai tsaya; kai dan uwana ne kuma tare za mu fatattaki talauci.”
"Duk wanda yake so zai iya yin takara, amma ba kowa ba ne zai iya zama shugaban kasa."

A nasa martanin Gwamna Aminu Masari ya amince cewa Najeriya na bukatar shugaba mai gogewa kan harkokin mulki.

Gwamnan na Katsina ya kuma bayyana imani da kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta shawo kan kalubalen da ke tunkarar ta nan ba da dadewa ba.

Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m

A wani labarin, wata kungiyar arewacin Najeriya da ta hada da Fulani makiyaya da al'ummar Almajirai, a ranar Litinin a Abuja ta ce ta shirya bai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan kuri'u miliyan 14 a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Kugiyoyin sun sanar da cewa sun siyar da shanunsu masu yawa domin tattara N100 miliyan na siyan masa fom din takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Idan za a tuna, a ranar Juma'a, 22 ga watan Afirilun 2022, wata kungiya ta tsinkayi ofishin tsohon shugaban kasan da ke Abuja inda ta bukace sa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.