2023: Jam’iyyun siyasa sun bukaci a sauya jadawalin zabe, INEC ta ce ba zai yiwuwa ba

2023: Jam’iyyun siyasa sun bukaci a sauya jadawalin zabe, INEC ta ce ba zai yiwuwa ba

  • Jam'iyyun siyasan kasar nan sun kai kuka ga INEC, sun bukaci a sake duba kundin zabe tare da yi masa kwaskwarima
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun ke gab da shiga wa'adin da hukumar zaben ta shar'anta na zaben fidda gwani
  • Sabon kudin zaben Najeriya ya tanadi sabbin abubuwa da dokoki da wasu 'yan siyasa ke ganin bai dace ba

Jam’iyyun siyasa sun bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta sauya jadawalin zaben 2023 domin ba da damar halartar zaben yadda ya kamata.

Musamman ma suka bukaci da a kara wa’adin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu da watanni biyu, The Nation ta ruwaito.

An roki hukumar zabe ta gyara jadawalin zabe
Da dumi-dumi: Jam’iyyun siyasa sun bukaci INEC da ta sauya jadawalin zaben 2023 | hOTOHoto: leadership.ng
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a bisa sabuwar dokar zabe ta sanya wa'adin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyun siyasa a ranar 3 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Duk da tanade-tanaden dokar zabe ta 2022, jam’iyyun siyasa 18 masu rajista karkashin inuwar majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) sun yi kira da a daidaita jadawalin zaben 2023.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da jadawalin zaben 2023 jim kadan bayan sanya hannu kan dokar zabe ta 2022.

Ta bukaci da a tsawaita wa'adin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar zuwa ranar 4 ga watan Agusta sabanin wa'adin da hukumar ta kayyade a ranar 4 ga watan Yuni, kamar yadda The Nation ta sake fitarwa.

Sai dai shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ba za a sake duba jadawalin zaben fidda gwani na jam'iyyun ba.

Ya tunatar da jam’iyyun siyasa cewa wa’adin da aka ware na gudanar da zaben fidda gwani ya fara ne a ranar 4 ga Afrilu 2022 kuma zai kare a ranar 3 ga Yuni 2022.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Bayan gaza biyan kudin Fam, Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC

A wani labarin, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adamu Garba, ya janye daga takarar saboda wasu dalilai.

A jawabin da ya saki a shafinsa ranar Talata a Abuja, Garba yace ya janye daga takarar ne saboda tsadar Fom din APC da kuma tsadar yin kamfe.

A cewarsa, sayar da Fam N100m zai maishe da siyasar Najeriya wajen cin kasuwa ne kawai ba shugabancin kwarai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel