Da duminsa: Bayan gaza biyan kudin Fam, Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC

Da duminsa: Bayan gaza biyan kudin Fam, Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC

  • Adamu Garba ya ce ya fasa sayan Fam din takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC
  • Garba ya ce kudin da jam'iyyar APC ta sanyawa Fom naira milyan dari zai halasta sata da rashawa a gwamnati
  • Yanzu, sun tara sama da naira milyan tamanin na gudunmuwa da wajen mutane

Birnin Abuja - Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adamu Garba, ya janye daga takarar saboda wasu dalilai.

A jawabin da ya saki a shafinsa ranar Talata a Abuja, Garba yace ya janye daga takarar ne saboda tsadar Fom din APC da kuma tsadar yin kamfe.

A cewarsa, sayar da Fam N100m zai maishe da siyasar Najeriya wajen cin kasuwa ne kawai ba shugabancin kwarai ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Yace ya yanke shawarar janyewa bayan shawara da kwamitin kamfensa kuma kawo yanzu sun samu N83.2 million sakamakon gudunmuwa daga wajen masoya.

Ya kara da cewa zai maida musu kudadensu.

Yace:

"A fahimtarmu wannan abu (tsadar kudin fom) zai mayar da siyasarmu wajen cin kasuwa, zai halasta sayen kuri'u, zai kara yawan rashawa da kuma kawar da matasa daga shiga siyasa."
"Lokacin da muka bayyana fahimtarmu wa yan jarida, jam'iyyar tace an yi tsadar Fam ne don sanin wadanda da gaske suke ko wasa."

Adamu Garba
Da duminsa: Bayan gaza biyan kudin Fam, Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC Hoto: @adamugarba
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

"Mun tara N81,750,000.00 na gudunmuwa da kuma N1,457, 794.70 na gudunmuwa daga yanar gizo. Jimilla N83,207,794.70."
"Muna matukar godiya ga dukkan wadanda suka bada gudunmuwa, har da wadanda suka ki bayyana sunayensu."

Jam'iyyar APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta rufe sayar da Fam din takara ga masu neman kujerar mulki karkashin lemarta a zaben kasa da za'a yi a 2023.

Jam'iyyar ta fara sayar da Fam din ne ranar 26 ga watan Afrilu, 2022.

A sabon jadawalin da jam'iyyar ta saki da daren Litnin, ta umurci dukkan wadanda suka karbi Fam su cike kuma su dawo da shi ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022.

Bayan haka ranar Juma'a za'a fara tantance Gwamnoni, yan majalisar wakilai, Sanatoci da shugaban kasa ranar Asabar, 14 ga Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel