Fom din takara N100m: NNPP za ta ba ku mamaki a zaben 2023, Kwankwaso ya yi kaca-kaca da APC

Fom din takara N100m: NNPP za ta ba ku mamaki a zaben 2023, Kwankwaso ya yi kaca-kaca da APC

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya magantu akan tsawwala kudin fom din takarar shugaban kasa da jam'iyyar APC ta yi
  • Kwankwaso ya nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyarsu ta NNPP za ta bayar da mamaki sosai a zabe mai zuwa
  • Ya bukaci masu aniyar tsayawa takara da su tafi sakatariyar NNPP domin yankan fom domin su basu tsawwala ba

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan siyar da fom dinta na shugaban kasa a kan naira miliyan 100, yana mai cewa fom din jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bai da tsada.

Kwankwaso wanda ya yi magana a taron shugannin NNPP na farko a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba irin APC bace wacce ta tsawwala kudin fom dinta na shugaban kasa har naira miliyan 100, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Fom din takara N100m: NNPP za ta ba ku mamaki a zaben 2023, Kwankwaso ya yi kaca-kaca da APC
Fom din takara N100m: NNPP za ta ba ku mamaki a zaben 2023, Kwankwaso ya yi kaca-kaca da APC Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Ya ce:

“Bari na tunatar da yan Najeriya cewa ana kan siyar da fom dinmu na kujerun majalisar dokoki ta jiha da sauran mukamai a sakatariyar jam’iyyar na kasa ga wadanda ke son takarar zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina son karfafawa kowa gwiwar zama kamar mu da muke nan; su zama mutane masu hangen nesa. Wannan jam’iyya duk ‘yan kishin kasa ne wadanda suka yi imani da kasar nan.
“Muna son kowa ya je ya yi rajista a unguwannin su. Fom din suna da arha sosai. Ba naira miliyan 100 bane na takarar shugaban kasa da sauransu."

Ya ba magoya bayansu tabbacin cewa NNPP za ta kutsa dukka yankunan kasar a babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Vanguard.

A halin da ake ciki, shugaban NNPP na kasa, Farfesa Rufai Alkali, ya bukaci kwamitin uwar jam’iyya da ta yi aiki tukuru domin samun nasara a babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Dubunnan ‘Ya ‘yan APC sun yi watsi da Jam’iyya mai mulki zuwa NNPP a jihar Zamfara

A cewar Alkali, Najeriya na bukatar a ceto ta daga hannun mugayen shugabanni da kuma dora ta ga turbar daukaka.

Kwankwaso: NNPP Za Ta Samu Gaggarumin Nasara a Zaɓukan 2023

A gefe guda, tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, za ta samu gaggarumin nasara a zabukan shekarar 2023.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Kwankwaso ya bada tabbacin ne ga magoya bayan jam'iyyar a yayin taron majalisar shugabannin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar a Abuja.

Kwankwaso, wanda ya ce yan Nigeria suna kara shiga jam'iyyar, ya shawarci saura su yi rajista kuma su nemi kujerar takara da suke so a zaben 2023 a karkashin jamiyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel