Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara

Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, da tsohon gwamnan da ya gada, Abdul-aziz Yari sun gyara saɓanin dake tsakanin su
  • Manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki sun garzaya wurin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, sun shaida masa APC ta ɗinke a Zamfara
  • Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC sabani ya ɓarke kan tsagin da zai tafiyar da jam'iyya

Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da tsohon gwamnan da ya gada, Abdul-Aziz Yari, sun gyara ɓarakar dake tsakanin su.

Hakan na ƙunshe ne a wani gajeren sako da jam'iyyar APC ta ƙasa ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Twitter ranar Litinin.

Yari, Adamu da gwamna Matawalle.
Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara Hoto: @OfficialAPCnig
Asali: Twitter

APC ta bayyana cewa manyan jiga-jigan biyu sun garzaya sun kai rahoto ga shugaban jam'iyya na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa sun warware sabanin dake tsakanin su.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Haɗin kan mutanen biyu na nufin kawo ƙarshen rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyya mai mulki reshen jihar Zamfara.

A gajeren sakon da APC ta fitar tare da Hotuna, ta ce:

"Gwamna Bello Matawalle da tsohon gwamna Abdul-Azizi Yari sun kawo rahoto ga shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, da sauran mambobin NWC cewa sun warware sabanin dake tsakanin su, hakan ya kawo karshen dogon rikicin APC a Zamfara.

Hotunan da APC ta fitar

Rikicin APC ya zo karshe a Zamfara.
Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara Hoto: @officialAPCNig
Asali: Twitter

Hotunan su Matawalle tare da Adamu.
Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara Hoto: @officialAPCNig
Asali: Twitter

Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga jam'iyyar PDP zuwa APC, aka samu ɓaraka tsakanin ƴaƴan jam'iyyar APC a Zamfara.

Bisa haka ne jam'iyyar da dare gida biyu, masu goyon bayan Yari da kuma waɗan da ke bayan Matawalle, wanda uwar jam'iyya ke goyon baya.

Kowane bangare ya gudanar da zaɓen shuwagabannin jam'iyya a matakai uku na jiha, amma APC ta ƙasa tsagin Matawalle ta yarda da shi, hakan ya sa lamarin ya kai ga Kotu.

Kara karanta wannan

Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu jiga-jigan FG su yi murabus

A wani labarin kuma Barau ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a 2023

Rikicin siyasa a jihar Kano kuma a jam'iyyar APC ya ƙara ɗaukar wani sabon babi tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje.

Sanata mai wakiltar Kano ta arewa kuma ɗan tsagin Shekarau ya sayi Fom ɗin takarar Sanata, wacce Ganduje zai nema a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel