'Hakurin mu ya kare' Ɗalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito zanga-zanga tsirara

'Hakurin mu ya kare' Ɗalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito zanga-zanga tsirara

  • Wasu tawagar ɗalibai mata sama da 500 sun shirya fara zanga-zanga kan titunan Bauchi rabin jikin su tsirara kan yajin aikin ASUU
  • Ɗaliban na jami'ar ATBU da kuma jami'ar jihar Bauchi sun ce sun ɗauki wannan matakin ne domin matsa wa a buɗe makarantu
  • Wannan na zuwa ne bayan ƙungiyar Malaman jami'o'i ASUU ta sanar da ƙara yajin aikinta da wata uku

Bauchi - Ɗalibai mata sama da 500 daga jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, da makociyarta Jami'ar jihar Bauchi, Gadau, sun shirya fitowa tituna zanga-zanga a faɗin jihar Bauchi rabin jikinsu tsirara.

Matan sun shirya fara wannan zanga-zanga ne biyo bayan ƙara wa'adin yajin aikin gargaɗi da kungiyar ASUU ta yi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Yajin aikin ASUU.
'Hakurin mu ya kare' Ɗalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito zanga-zanga tsirara Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin ɗalibai matan da suke jagorantar shirya zanga-zangar wacce ta nemi a ɓoye bayananta ta ce:

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

"Zuwa yanzun mun tuntuɓi ɗalibai mata 500 kuma sun amince zasu shiga zanga-zangar, muna tsammanin samun ƙari kafin ranar ƙarshe."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A matsayin mu na ɗalibai ma su bin doka, mun jima muna hakuri, goben mu na cikin hatsari saboda wasu tsirarun yan ƙasa da ba abun da ya dame su sai 'ya'yan su da iyalan su."

Ta ce zasu bi duk wasu hanyoyin da doka ta tanada wajen matsa wa bangarorin biyu lamba don tabbatar da an buɗe jami'o'in Najeriya nan gaba kaɗan.

Yajin aikin ASUU a 2022

A tsakiyar watan Fabrairu, kungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa ASUU ta sanar da shiga yajin aiki na mako huɗu bisa hujjar gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar.

A watan Maris, ASUU ta ƙara tsayin yajin aikin da wata biyu, inda ta ce gwamnati ba da gaske take ba wajen shawo kan abubuwan da kungiyar ke fafutuka a kai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Bayan ɗalibai sun sake shafe watannin a gida, ƙungiyar ta sake tsawaita yajin aikim da makonni 12 a cikin wannan watan da muke ciki na Mayu.

A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel