Da Dumi-Dumi: Barau ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a 2023

Da Dumi-Dumi: Barau ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a 2023

  • Rikicin siyasa a jihar Kano kuma a jam'iyyar APC ya ƙara ɗaukar wani sabon babi tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje
  • Sanata mai wakiltar Kano ta arewa kuma ɗan tsagin Shekarau ya sayi Fom ɗin takarar Sanata, wacce Ganduje zai nema a 2023
  • Barau Jibrin ya haƙura da neman kujerar gwaman jihar Kano ya fara shirin neman tazarce a kan kujerarsa ta Sanata da yake kai

Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta arewa, Sanata Barau I Jibrin, ya janye takarar gwamnan jihar Kano kuma ya Sayi Fom Fom ɗin tazarce a kujerarsa ta sanata.

Biyo bayan faruwar haka, Sanata Barau zai ƙalubalanci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda masu ruwa da tsaki na Kano suka goyi bayan ya nemi kujerar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Gwamna Ganduje da Sanata Barau.
Da Dumi-Dumi: Barau ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai fafata da Ganduje a 2023 Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

Barau, wanda ake kallon ya na ɗaya daga cikin manyan masu neman takarar gwamnan Kano, ya janye ne awanni 24 bayan Ganduje ya bayyana wanda ya ke son ya gaje shi.

Gwamna Ganduje, wanda wa'adin mulkinsa zango na biyu zai ƙare a 2023, ya zaɓoi mataimakonsa ya zama ɗan takarar masalaha da zai gaji kujerarsa ƙarƙashin APC.

Wata majiya ta bayyana cewa ɗan majalisa dattawan ya rinjayi shugabannin APC a Kano kan batun janye takara da kuma yunkurin neman sake komawa majalisar dattawa.

Sanata Barau ya na ɗaya daga cikin jagororin tsagin jam'iyyar APC da ake wa laƙabi da G7, wacce tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau, ke jagoranta.

Sanara Barau Jibrin, a wata tattauna wa ta wayar salula, ya tabbatar da cewa ya karɓi Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara domin tazarce a kan kujerar Sanata.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

A wani labarin kuma Gwamna ya faɗi dalilin da ya hana shi fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin yan bindiga a jiharsa ba

Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ce hukumomin tsaro ne suka buƙaci karin lokaci shiyasa bai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin yan bindiga ba.

Ya ce karo na karshe da suka tattauna sun bukaci ya ƙara musu mako biyu, bayan haka ya ce zai sanar da yan Najeriya sunan mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel