Kada ku barnata kuri'unku, kawai ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC

Kada ku barnata kuri'unku, kawai ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC

  • Gabannin zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, ministan sufuri ya yi gagarumin kira ga wakilan jam'iyyar
  • Amaechi ya shawarci wakilan da kada su yi asarar kuri'unsu wajen zabar mutumin da bai cancanta ba domin daga tutar jam'iyyar a zaben shugaban kasa na 2023
  • Ya ce duk wanda ya kawo masu kudi don su zabe shi su karbi abun su amma su duba cancanta wajen kada kuri'unsu

Edo - Ministan sufuri kuma mai son zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Amaechi, ya ce zabarsa a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar ba zai zama asarar kuri’u ba.

Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, a yayin da yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar Edo, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Ya bukaci wakilan da su mayar da hankali wajen zabar dan takarara irinsa wanda ya cancanta domin daga tutar jam’iyyar.

Kada ku barnata kuri'unku, ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC
Kada ku barnata kuri'unku, ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Nigerian Tribune ta nakalto Amaechi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yan siyasa za su zo don neman kuri’unku, amma dan Allah, a matsayinku na mutanen kudu maso kudu, a matsayinku na yan siyasa, a matsayinku na mutanen Najeriya masu nagarta, kada ku yi asarar kuri’unku.
“Matsalar yan siyasa kune. Shugabanni sun nuna maku cewa sun zo nan don cin kudi ne sannan kuka kyale su. Za su kawo kudi nan sannan su ce ku zabe su, sannan babu wanda zai damu da tambayar ‘menene shi kafin yanzu? ‘menene bajintarsa? ‘tattalin arzikin da suke so su zo su kula da shi, wani bajinta suka yi?
“Zaben dan takara yana da mahimmanci a gare ku. Idan ba haka ba, APC za ta fadi zabe. A yanzu, ina tsammanin ni ne nafi cancanta, an gwada ni kuma an amince da ni.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

“Idan suka tambayeni, ina da gagarumin hujja- makarantun firamare na gwamnati, makarantun sakandare, cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati, asibitoci, hanyoyi, wutar lantarki mai karfin megawatt 750 a jihar Ribas, an tura yara kasashen waje karatu, an dauki malamai 13,200 aiki, da sauran nasarori a matsayin gwamna.
“A matsayin ministan sufuri, na kammala hanyar layin dogo na Kaduna zuwa Abuja, sannan na Lagas zuwa Ibadan na aiki. Ga wadanda ke cewa, ‘me ya yiwa kudu maso kudu? Akwai layin dogo na Warri-Itakpe; garuruwa biyu ne kadai ke a Kogi, sannan sauran na jihohin Edo da Delta ne.
“Mun fara layin dogo na Fatakwal zuwa Maiduguri, kuma za mu fara layin dogo daga Legas zuwa Calabar. To, da suka ce ‘Bai yi komai a Kudu maso Kudu’ ba, shin suna nufin cewa Delta da Edo ba sa cikin Neja-Delta?
“Ina da shaidar irin gudunmawar da nake bayarwa ga APC da Najeriya. Zan iya lissafa tsawon lokacin da na shafe a ofis. Don haka in sun kawo kudi su karba, amma mu tashi mu yi zabe daidai, mu kare kuri’unmu.”

Kara karanta wannan

Wani dan takarar shugaban kasa ya karaya ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

2023: Abun mamaki ne yadda yan takarar APC ke son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya – Wike

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi mamakin wani irin kyawawan ayyuka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wanda har yasa masu neman darewa kujerarsa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke daukar alkawarin dorawa a kansu.

Wike, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ce yan Najeriya a karkashin gwamnatin APC na fama da matsalar tsaro wanda ya gurguntar da tattalin arziki da haddasa yunwa, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel