Lokaci ya yi da za mu kwato Najeriya daga hannun mazan jiya - Saraki

Lokaci ya yi da za mu kwato Najeriya daga hannun mazan jiya - Saraki

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya magantu a kan halin da kasar ke ciki a yanzu
  • Saraki ya bayyana cewa lokaci ya yi da yakamata yan Najeriya su kwato kasarsu daga hannun mazan jiya wadanda basa nufinsu da alkhairi
  • Dan siyasar wanda ke neman gaje Buhari a 2023 ya ce idan har aka zabe shi toh zai farfado da tattalin arzikin kasar tare da fitar da ita daga matsalolin da take fuskanta

Kaduna - Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ya kamata yan Najeriya su karbe kasarsu daga hannun mazan jiya wadanda basa nufinsu da alkhairi.

Ya yi zargin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata da alkibla da karfin magance tarin matsalolin da ke fuskantar kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Lokaci ya yi da za mu kwato Najeriya daga hannun mazan jiya - Saraki
Lokaci ya yi da za mu kwato Najeriya daga hannun mazan jiya - Saraki Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Saraki wanda ya zanta da wakilan PDP a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, a jihar Kaduna gabannin zaben fidda gwanin jam’iyyar, ya ce yayin da yake shugaban majalisar dattawa, sau da yawa ya ki amincewa da bukatun fadar shugaban kasa na ciyo wa yan Najeriya basussuka marasa dalili.

Ya yi alkawarin kawo karshen matsalar rashin tsaro idan har aka bashi tikitin shugaban kasa na jam’iyyar, yana mai cewa yaran wannan kasa basa iya zuwa makaranta hankali kwance, yayin da manoma ke tsoron zuwa gona saboda tabarbarewar rashin tsaro a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya caccaki APC kan haddasa wahala ga yan Najeriya.

Ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya, gina ababen more rayuwa da daidaita kasar kan tafarkin ci gaba, rahoton Thisday.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya koka kan rashin alkibla da karfi daga wannan gwamnati don magance matsalolin da ke fuskantar kasar.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

“Ina baku tabbaci a matsayina na likita wanda ke magance matsaloli bayan gano tushensa, zan fuskanta tare da sa himma sosai wajen kawo karshen matsalolin kasar nan.
“Zan samar da yanayi mai kyau ta yadda za a tallafa wa matasanmu masu tasowa su yi fice a fagen da suka zaba.
“Ba a taba samun rabuwar kai a Najeriya ba kamar yadda muke gani a yau kan addinai da kabilanci, zanyi iya bakin kokarina don tabbatar da ganin cewa na hada kan mutanen kasar nan masu karamci.
“An haife ni bayan samun yancin Najeriya kuma na fahimci kalubalen da ya biyo bayan samun yancin kanmu wanda wannan jam’iyyar mai mulki ta hada.
“Lokaci ya yi da ya kamata mu kwato kasarmu abun sonmu daga wadannan mazan jiyan wadanda basa nufinmu da masu tasowa da alkhairi.”

A kullun Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa – Gwamna Badaru

A wani labari na daban, Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa.

Kara karanta wannan

Idan na zama shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai sake biyan kudin asibiti: Saraki

Badaru wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnonin APC, ya bayyana hakan ne a yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today.

Badaru ya kara da cewa a 2023 yan Najeriya za su sake zabar APC saboda suna da tarihin abun da PDP ta yiwa kasar, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel