Idan na zama shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai sake biyan kudin asibiti: Saraki

Idan na zama shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai sake biyan kudin asibiti: Saraki

  • Bukola Saraki ya lissafo jerin alkawuransa ga yan Najeriya idan suka zabesa ya zama shugaban kasa a 2023
  • Saraki na cikin jerin yan takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP
  • Saraki ya yi gwamna sau biyu a jihar Kwara kuma ya zama shugaban majalisar dokokin tarayya a 2015

Kaduna - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa idan yan Najeriya suka zabesa, zai kawo karshen matsalar tsaro, yunwa, da rashin aikin yi.

Saraki, wanda dan takara ne karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yace a mtsayinsa na Likita, ba dan Najeriyan da zai sake biyan kudin jinya a asibiti.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa deleget din jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, rahoton TheNation.

Yace:

"Idan na zama shugaban kasa, zan magance matsalar rashin tsaro. Zan farfado da masaka da kamfanonin mai. Kuna bukatar mutumin da ake ganin girmansa a gida da waje."

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

"A matsayina na Likita, zan tabbatar da cewa babu wanda ya sake biyan kudin asibiti. Wannan zai yiwu kuma zamuyi Insha Allah."

A Kaduna, Saraki ya ziyarci tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmad Makarfi, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Namadi Sambo, don neman goyon bayansu.

Saraki
Idan na zama shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai sake biyan kudin asibiti: Saraki

Bukola Saraki ya ziyarci Obasanjo kan batun takarar shugaban ƙasa a 2023

Sanata Bukola Saraki, ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Saraki, wanda ke neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP, ya dira gidan Obasanjo ne dake harabar Laburarin sa (OOPL) da misalin ƙarfe 12:04 na tsakar rana yau Litinin.

Daily Trust ta rahoto cewa ya dira tare da yan tawagarsa da suka haɗa da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Kawu Baraje, da sauran su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel