Da Ɗumi-Ɗumi: Bayan Jobe, Wani Ɗan Majalisar Kano Ya Sake Fita Daga APC
- Alhassan Rurum, Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, kuma dan majalisar tarayya mai wakiltan Rano/Bunkure/Kibiya ya fita daga APC
- Ficewar Rurum na zuwa ne bayan dan majalisar jihar Kano Abdullahi Jobe shima ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ta APC mai mulki yana mai cewa rikicin jam'iyyar ta sa ya fita
- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Rurum ya fita daga APC ne kan zargin rashin adalci bayan Gwamna Ganduje ya zabi Nasir Gawuna da Murtala Sule-Garo su gaji shi
Jihar Kano - Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhassan Rurum, ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress, APC, Premium Times ta ruwaito.
Rurum, wanda a yanzu shine ke wakiltan mazaban Rano da Bunkure da Kibiya a majalisar wakilai na tarayya, yana daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna a APC.
Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP
Amma, ya cire rai da hakan bayan masu ruwa da tsaki a yau Lahadi karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje sun zabi mataimakin gwamna Nasir Gawuna da tsohon Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule-Garo a matsayin mataimakin gwamna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Ba a yi wa al'ummar Kano ta Kudu adalci ba'
A cewar wasu majiyoyi, tsohon kakakin majalisar yana ganin cewa shugabannin jam'iyyar ba su yi wa al'ummar Kano ta Kudu adalci ba, domin zaben Gawuna daga Kano ta Tsakiya sai Gari daga Kano ta Arewa, rahoton Daily Trust.
Kano ta Kudu bata taɓa fitar da gwamna ba ko mataimaki tun shekarar 1992. 'Yan siyasa daga yankin sun yi zaton za a basu dama a 2023.
Amma, Rurum ya shaidawa yan jarida cewa yana tuntubar masu ruwa da tsaki game da jam'iyyar da zai koma, yana mai cewa zai sanar nan gaba.
Rikicin APC a Kano: Ɗan Majalisa, Abdulkadir Jobe Ya Fice Daga Jam'iyyar APC, Ya Bayyana Dalili
Tunda farko, kun ji cewa, Dan majalisar wakilai na tarayya daga Jihar Kano, Abdulkadir Jobe, ya yi murabus daga jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, Premium Times ta rahoto.
Mr Jobe, wanda ke wakiltar mazabun Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa ya ce ya fice daga jam'iyyar ne saboda rikicin cikin gida da ake yi a jam'iyyar reshen Kano.
Amma, bai bayyana cewa ko zai shiga wata jam'iyyar siyasar ba. Sai dai, an ga hotonsa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP bayan wata ziyara da ya kai masa a ranar Juma'a a gidansa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng