2023: Abun mamaki ne yadda yan takarar APC ke son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya – Wike

2023: Abun mamaki ne yadda yan takarar APC ke son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya – Wike

  • Gwamna Nyesom Wike ya nuna mamakinsa kan yadda yan takarar shugaban kasa na APC ke cewa za su ci gaba daga inda Shugaba Buhari ya tsaya
  • Wike ya ce Allah ba zai sa magajin shugaban kasar ya zama irinsa ba domin yan Najeriya sun wahala
  • Ya ce babu wani kyakkyawan aiki da wannan gwamnati ta yi face matsalar tsaro, talauci, yunwa da koma bayan tattalin arziki da kasar ke fama da su

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi mamakin wani irin kyawawan ayyuka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wanda har yasa masu neman darewa kujerarsa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke daukar alkawarin dorawa a kansu.

Wike, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ce yan Najeriya a karkashin gwamnatin APC na fama da matsalar tsaro wanda ya gurguntar da tattalin arziki da haddasa yunwa,rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

2023: Abun mamaki ne yadda yan takarar APC ke son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya – Wike
2023: Abun mamaki ne yadda yan takarar APC ke son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya – Wike Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da yake magana a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa a ranar Juma’a a yayin da ya gana da Gwamna Douye Diri a gidan gwamnati, Wike ya ce Allah da yan Najeriya ba za su bari irin wannan magajin ya bayyana ba.

Ya ce ya zama dole kasar ta tsira daga rashin tsaro, yunwa, talauci da durkushewae tattalin arziki da mutanenta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Kelvin Ebiri, hadimin gwamnan zuwa ga manema labarai a Port Harcourt.

Wike ya ce:

“Abun takaici ne idan na ji mutane na ayyana kudirinsu na son takarar shugaban kasa a APC suna sannan suna fadin cewa suna so su ci gaba da kyakkyawan aikin Shugaban kasa - kyakkyawan aikin da mutane ke mutuwa a kullun, kyakkyawan aikin da darajar naira ke faduwa a kullun.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

“Ina jin kunya sosai cewa mun kai matakin da mutane za su fito suna cewa Ina so na ci gaba da kyakkyawan aikin Buhari. Menene kyakkyawan aikin Buhari - yunwa, talauci, rashin tsaro, durkushewar tattalin arziki?

“Na yi mamakin cewa wani zai fito a yau a Najeriya sannan ya ce Ina son ci gaba daga inda Buhari ya tsaya. Kada Allah ya bari wannan muguntan ya ci gaba.

Wike ya bayyana kansa a matsayin shugaba mafi kwarin gwiwa wanda zai iya fitar da Najeriya daga mawuyacin halin da take ciki.

Ya bukaci takwaransa na jihar Bayelsa da ya marawa kudirinsa baya, yana mai cewa yana son yin takara a madadin jihohin biyu.

2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar

A wani labari na daban, babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya saka baki domin magance rikicin siyasa tsakanin Abdulmumin Jibrin da manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban Najeriya sun gano mafita, za su tara wa lakcarori kudi kawai

A ranar Asabar, 7 ga watan Mayu ne Jibrin ya sanar da hukuncinsa na barin jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya da bai bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel