Mataimakiyar gwamnan Kaduna ta janye takararta, ta marawa dan takarar da El-Rufai ke so baya

Mataimakiyar gwamnan Kaduna ta janye takararta, ta marawa dan takarar da El-Rufai ke so baya

  • Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr Hadiza Sabuwa Balarabe, ta janye daga tseren kujerar gwamna a zaben 2023
  • Hadiza ta nuna goyon bayanta ga takarar Sanata Uba Sani wanda shine zabin Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin dan takarar maslaha
  • Sai dai kuma, majiya ta bayyana cewa mataimakiyar gwamnan ta yi watsi da tayin da aka yi mata na zama abokiyar takarar Uba Sani a zaben

Kaduna - Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr Hadiza Sabuwa Balarabe, ta nuna goyon bayanta ga dan takarar gwamna da Nasir El-Rufai ke goyon baya.

A ranar Laraba da ta gabata ne El-rufai ya lamuncewa Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar APC a zaben 2023.

An tattaro cewa an yiwa mataimakiyar gwamnan, wacce ke cikin jerin manyan yan takara uku da ke neman maye gurbin gwamnan jihar Kaduna tayin zama abokiyar takarar Uba Sani amma ta yi watsi da hakan.

Kara karanta wannan

Hadiza Sabuwa Balarabe, wasu mata 3 da ke rike da matsayin Mataimakin Gwamna a yau

Mataimakiyar gwamnan Kaduna ta janye takararta, ta marawa dan takarar da El-Rufai ke so baya
Mataimakiyar gwamnan Kaduna ta janye takararta, ta marawa dan takarar da El-Rufai ke so baya Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Sai dai kuma a wani mataki da masana suka bayyana a matsayin dabarar gyara, mataimakiyar gwamnan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta nuna goyon bayanta ga hukuncin El-Rufai tare da yin kira ga magoya bayanta da su marawa jam’iyyar APC baya a dukkan matakai a zaben 2023 mai zuwa, Daily Trust ta rahoto

Ta ce:

‘Ina son mika godiya ta musamman ga mai girma Mallam Nasir Ahmad El-Rufai bisa amincewa da kuma yarda da yayi da ni a matsayin abokiyar takararsa/mataimakiyarsa.Na yi imani ayyukansa a wannan lokacin ba su bar kowa cikin shakkar cewa ya amince da ni ba. Wadannan damammaki ne da ba zan manta da su ba har abada, kuma zan kaunata da rike shi har iya tsawon rayuwata."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Daily Trust ta tattaro cewa Balarabe ta yi watsi da tayin da El-Rufai ya yi mata a gaban sauran manyan yan majalisarsa a cikin makon.

Wani makusancinsa ya fada ma jaridar cewa duk da dabarar da ta yi na kin amsar tayin, hakan bai yi masu dadi ba.

Ya ce:

“Wannan wata hanya ce ta gyara saboda wasu mutane sun fara yayata cewa akwai Baraka a majalisar El-Rufai kuma ya kamata ta tabbatar da cewar iyalai daya ne.”

A cikin jawabinta, mataimakiyar gwamnan ta yabawa mutane, kungiyoyin matasa, kungiyoyin mata, kungiyoyin dattawa da kungiyoyin Kirista da na musulmai wadanda suka daga muryoyinsu sannan suka sadaukar da dukiyoyinsu don nuna mata goyon baya don ganin ta shiga tseren kujerar gwamna a 2023.

Ta Bayyana: Sabbin Bayanai Kan Ainihin Dalilan Da Yasa El-Rufai Ya Zaɓi Uba Sani Ya Gaje Shi

A gefe guda, sabbin bayannai sun bayyana dangane da dalilin da yasa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya zabi Sanata Uba Sani (APC, Kaduna Central) a matsayin wanda ya ke son a bawa tikitin takarar gwamna na APC, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

A ranar Alhamis ne Daily Trust ta wallafa rahoton cewa gwamnan ya nuna goyon bayansa ga dan majalisar a matsayin magajinsa.

Hakan na zuwa ne bayan rahoton da aka wallafa a ranar 13 ga watan Maris, inda aka bayyana sunayen wadanda ke aiki kut-da-kut da El-Rufai ciki har da Uba Sani. Gwamnan dama ya ce a cikinsu zai zabi magajinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel