Ta Bayyana: Sabbin Bayanai Kan Ainihin Dalilan Da Yasa El-Rufai Ya Zaɓi Uba Sani Ya Gaje Shi

Ta Bayyana: Sabbin Bayanai Kan Ainihin Dalilan Da Yasa El-Rufai Ya Zaɓi Uba Sani Ya Gaje Shi

  • Bayanai sun fito dangane da dalilan da yasa Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya zabi Sanata Uba Sani a matsayin magajinsa
  • Tun a baya dama El-Rufai ya ce ba zai tursasa wa jam'iyya dan takara ba amma dai a zuciyarsa akwai wanda ya fi ganin ya fi dacewa cikin mukusantarsa da ya ke aiki da su
  • Bayanai daga majiya da ke kusa da El-Rufai ta nuna cewa an yi kididdiga ne kuma alkalluma suka nuna Uba Sani ne zai fi karbuwa a wurin talakawa kuma ya ci zaben

Sabbin bayannai sun bayyana dangane da dalilin da yasa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya zabi Sanata Uba Sani (APC, Kaduna Central) a matsayin wanda ya ke son a bawa tikitin takarar gwamna na APC, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

A ranar Alhamis ne Daily Trust ta wallafa rahoton cewa gwamnan ya nuna goyon bayansa ga dan majalisar a matsayin magajinsa.

Ta Bayyana: Ainihin Dalilan Da Yasa El-Rufai Ya Zabi Uba Sani Ya Gaje Shi
Ainihin Dalilan Da Yasa El-Rufai Ya Zabi Uba Sani Ya Gaje Shi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne bayan rahoton da aka wallafa a ranar 13 ga watan Maris, inda aka bayyana sunayen wadanda ke aiki kut-da-kut da El-Rufai ciki har da Uba Sani. Gwamnan dama ya ce a cikinsu zai zabi magajinsa.

Mutane 10 sun hada a mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe, Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas Lawal, Kwamishinoni uku - Bashir Saidu (Kudi), Muhammad Sani Abdullahi (Kasafi da Tsare-Tsare) da Samuel Aruwan (Tsaron cikin gida).

Saura sun hada da Sanata Sule Kwari (Kaduna North) Jimi Lawal (Senior Adviser Councillor), Hafiz Bayero (Shugaban Kaduna Municipal Authority) Muyiwa Adeleke (SA Media) da Saude Atoyebi (Mataimakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamna).

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

An gano cewa mutum uku daga cikinsu da suka hada da Uba Sani, Hadiza Balarabe da Mohammed Sani Abdullahi, da aka fi sani da Dattijo suna cikin wadanda aka duba yiwuwar zabensu.

Wata majiya kusa da gwamnan ta ce sunan Sani ne ya yi fice a kiddiga da aka yi da dama domin gwada 'karbuwarsu wurin al'umma, gogewa, wayewa, da saukin tallatawa' cikin su ukun.

Bayan sakamakon kiddidigan, an kira dukkan makusanta gwamnan taro inda aka zabi Sani a matsayin dan takara na sasanci.

Majiyar ta ce:

"Gogewarsa a matsayin mashawarci a gwamnatin Obasanjo, mashawarci na siyasa ga Gwamna El-Rufai da ayyukan da ya yi a matsayinsa na sanata suka sa ya samu goyon bayan gwamnan.
"Masu ruwa da tsakin suna son wanda ya fi dacewa cikin mutanen uku don APC ta yi zaben fidda gwani a matsayinta na tsintsiya madaurinki daya. Duk da sauran yan takarar biyu sun taka rawar a zo a gani cikin shekaru bakwai da suka gabata, Sani ya fi samun goyon bayan talakawa," in ji shi.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Wani majiya daga jam'iyyar ya ce Sani ne wanda APC ke ganin zai cin zaben.

"Muna bukatar dan takara mai farin jini idan muna son cin zabe. Mataimakiyar gwamna da Dattijo kusan sabon shiga ne a harkar siyasa."

Ya kuma ce Sani ya tallafawa gwamnatin jihar a bangarori da dama a matsayinsa na dan majalisar tarayya.

"Shugaban kasa ya amince da kudi biyu cikin 21 da aka gabatar a majalisa. Ta dalilinsa ne aka samu kudin gina tsangayar koyon karatun Injiniya a Jami'ar Kaduna, KASU," in ji shi.

An gano cewa tawagar ta yi shawara cewa mataimkiyar gwamnan za ta cigaba da rike kujerarta, Dattijo zai yi takarar sanata kuma Sanata Suleiman Kwari na Kaduna North zai cigaba da rike kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel