Kaduna 2023: Za Mu Amince Da Kama Karya Ba, Ɗan Takarar Gwamna, Sha'aban Ya Yi Watsi Zaɓin El-Rufa'i

Kaduna 2023: Za Mu Amince Da Kama Karya Ba, Ɗan Takarar Gwamna, Sha'aban Ya Yi Watsi Zaɓin El-Rufa'i

  • Wani dan takarar gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Sani Sha’aban ya nuna rashin amincewarsa da dan takarar da Nasir El-Rufai ya mara wa baya
  • Dama tun ranar Laraba El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna sannan ya nemi Muhammad Sani Dattijo ya tsaya a takarar sanata
  • Sha’aban ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da shi a gidansa cikin ranakun karshen mako

Kaduna - Alhaji Sani Sha’aban, wani dan takarar gwamna a Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC ya nuna rashin amincewarsa da dan takarar gwamnan da Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya mara wa baya a zaben 2023 da ke karatowa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Sha’aban ya bayyana hakan ne yayin da manema labarai su ke tattaunawa da shi a gidansa cikin kwananin karshen mako, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kaduna 2023: Za Mu Amince Da Kama Karya Ba, Ɗan Takarar Gwamna, Sha'aban Ya Yi Watsi Zaɓin El-Rufa'i
Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Sha’aban ya ki amincewa da dan takarar da El-Rufai ya mara wa baya. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba, El-Rufai ya zabi Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar da ya mara wa baya don tsayawa takarar gwamna, inda ya nemi Muhammad Sani Dattijo, dayan dan takarar da ya siya fom din sanata.

Sai dai kamar yadda Nigerian Tribune ta nuna, yayin da Sha’aban ya samu labarin nan, ya nuna rashin amincewarsa da zabin da El-Rufai ya yi.

Ya bukaci sanin ko su wanene wadanda su ka ba gwamna damar daukar matakin da ya yi, a matsayinsa na wadanda su ka kafa jam’iyyar a iya saninsa, babu wanda ya neme shi kafin a dauki matakin.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Tuɓe Rawanin Sarki Saboda Ya Halarci Taron PDP

A cewarsa:

“Ina daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APP daga nan ta koma ANPP, bayan ta yi maja da wasu jam’iyyu uku a yau aka mayar da ita APC.”

Ya bayyana mamakinsa akan yadda aka dauki matakin kai tsaye ba a tuntube shi ba

Dangane da zaben dan takarar da gwamnan ya yi, Sha’aban wanda sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ci gaba da cewa:

“Mun yi mamakin yadda aka yanke wannan hukuncin a Jihar Kaduna da ta ke da fiye da mutane 3m masu zabe ba tare da tuntubar wasu daga cikinmu ba wadanda su ka siya fom din takara da wuri.
“Demokradiyya batun ra’ayi ne, kuma batu ne na kowa ya nuna zabin da ke ransa, mun yarda da cewa akwai lauje cikin nadi a wannan matakin da gwamnan Jihar Kaduna ya yi.
“Sai dai idan bayan kwashe shekaru 8 a APC, ba sa fatan ci gaban APC da kuma Jihar Kaduna. In har sun damu da ci gaban jam’iyyar, da kuma damuwar mutanen Jihar Kaduna, kuma sun damu da sakon Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin APC na abubuwan su ka ce da aka zabe su bayan gama gangami, na kawo hadin kai da ci gaba, bai dace su yi hakan ba.”

Kara karanta wannan

Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

Ya ce ya cancanci sanin halin da ake ciki a jam’iyyar ko da ta wayar salula ne

Tsohon dan majalisar wakilan ya ce zai cikashe fom din shi kuma ya mayar da shi yadda ya dace yayin da zai jira ya ji umarnin da jam’iyya za ta bayar.

Ya ci gaba da cewa bai amince da zaben Sanata Uba Sani da aka yi ba a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Kaduna ba a zaben 2023.

Ya ce har sai sun jira sun ga sakamakon zaben fidda gwani tukunna don ba za a mayar da su kamar hoto ba.

A cewarsa ya na da hakkin da ya dace a sanar da shi duk wani abu da za a yi ko da kuwa ta wayar salula ne. Idan aka mayar da shi banza, shi ma yana mayar da mutum banza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel