Gwamnan APC Ya Tuɓe Rawanin Sarki Saboda Ya Halarci Taron PDP

Gwamnan APC Ya Tuɓe Rawanin Sarki Saboda Ya Halarci Taron PDP

  • Ben Ayade, Gwamnan Jihar Cross River, ya tube rawanin Itam Hogan Itam, wani basarake da ke karamar hukumar Calabar ta kudu akan shiga sha’anin siyasa
  • An samu bayanai dangane da yadda Itam ya je taron jam’iyyar PDP wanda su ka mara wa Arthur Jarvis baya a matsayin dan takarar gwamnan jihar na zaben 2023
  • A takardar ranar 11 ga watan Mayu wacce hadimin gwamnan na harkar sarauta, Adoga Victor ya sanya hannu, an umarci Itam ya yi gaggawar mayar da satifiket din sarauta ga ofishin gwamnatin jihar

Cross River - Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade ya tube rawanin Itam Hogan Itam, basaraken yankin Calabar ta kudu akan shiga harkar siyasa dumu-dumu, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

An ruwaito yadda Itam ya je taron mazabar kudancin jihar na jam’iyyar PDP inda aka samu labarin an zabi Arthur Jarvis a matsayin dan takarar gwamnan jihar na zaben 2023.

Gwamnan APC Ya Tuɓe Rawanin Sarki Saboda Ya Halarci Taron PDP
Gwamna Ayade Ya Tuɓe Rawanin Sarki Saboda Ya Halarci Taron PDP. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Donald Duke, tsohon gwamnan jihar ne ya shirya taron.

Zuwa taron da basaraken ya yi ya ci karo da dokar sarautar gargajiyar Jihar Cross River.

Wata takarda ta ranar 11 ga watan Mayu wacce Adoga Victor, hadimin gwamnan na musamman na harkar sarauta ya sanya hannu, an umarci Itam da ya mayar da satifiket din sarauta ga ofishin gwamnatin jihar, ta bangaren harkokin sarauta.

Ayade ya hakura da tsayawa takarar shugaban kasa, zai mara wa Goodluck Jonathan baya

Kamar The Punch ta rahoto nuna, takardar ta bayyana cewa:

“Bayan samun rahoto daga kwamitin da majalisar Shugabannin Gargajiyar Jihar Cross River, CRSTRC, ta shirya, an tube ka a matsayin dagacin kauyen Ukem kuma shugaban Efuts don a ba ka damar zuwa yin harkokinka na siyasa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Sanata Hayatu Gwarzo, ya zama mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma

“Don haka daga yanzu an cire ka kuma ba za ka ci gaba da rike kujerar ba.”

Ayade ya na cikin ‘yan siyasar APC wadanda su ka nuna kudirinsu na tsayawa takarar shugaban kasa.

Sai dai gwamnan ya ce zai hakura da neman kujerar don mara wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan baya, idan har ya zabi tsayawa takara karkashin jam’iyyar APC.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel