2023: Gwamnan APC ya ba Buhari shawarar tsige Gwamnan CBN idan bai janye takara ba

2023: Gwamnan APC ya ba Buhari shawarar tsige Gwamnan CBN idan bai janye takara ba

  • Oluwarotimi Akeredolu ya tsoma baki a game da takarar da Godwin Emefiele yake shirin yi a 2023
  • Gwamna Akeredolu ya bukaci Gwamnan nan CBN ya sauka daga mukaminsa idan yana son takara
  • Idan Emefiele ya ki yin murabus daga bankin, Gwamnan ya ba shugaban kasa shawarar ya shige shi

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya fadawa shugaban kasa ya tsige Godwin Emefiele idan ya cigaba da neman shugabancin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya yi wannan kira ne jim kadan bayan gwamnan na CBN ya yanki fam din tsayawa takara a APC.

Godwin Emefiele ya saye fam din neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, a lokacin da ya ke rike da shugabancin babban bankin kasa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

Akeredolu ya fitar da wani jawabi na musamman a ranar Juma’a 6 ga watan Mayu 2022, yana ba Muhammadu Buhari shawara ya fatattaki gwamnan na CBN.

A cewar Gwamnan, muddin Emefiele bai ajiye aikinsa ba, ya cigaba da takara, to shiriritar tayi yawa.

Punch ta rahoto Akeredolu yana kokawa da cewa an dade ana rade-radin gwamnan babban bankin zai kutsa siyasa, an ga hotunan motocin yakin zabensa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr. Godwin Emefiele
Gwamnan babban banki, Godwin Emefiele Hoto: Chris J. Ratcliffe/Bloomberg
Asali: Getty Images

A cewar Mai girma gwamnan, hankalin mutane bai kwanta da masu marawa Emefiele baya ba.

Jawabin Rotimi Akeredolu SAN

“Sabon labrin da ake ji ya tabbatar cewa Gwamnan (CBN) ya jefa kan shi a cikin siyasa kamar duk wani mai ra’ayin harkar siyasa a Najeriya.”
“Shakka babu, dokar kasa ta ba Emefiele dama ya shiga duk wata kungiya kamar kowane ‘dan kasa. Amma bai dace ga irin gwamnan CBN ba.”

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

“Ba sai an fada ba, tsarin aikin gwamnati da dokar CBN da kundin tsarin mulkin 1999 sun haramta wannan yunkuri na takara yayin da yake ofis.”
“A dalilin haka, mu na kira ga Mista Emefiele ya yi gaggawan sauka daga kujerarsa domin ya cin ma burin siyasarsa, ba zai hada takara da rikon CBN ba.”
“Idan zai ki ajiye kujerar gwamnan CBN, ya zama dole shugaban kasa ya tsige shi bayan haka.”

- Rotimi Akeredolu SAN

Onu ya ayyana shirin takara

A ranar Juma'a ne aka ji Ministan kimiyya da fasaha ya shiga takara. Dr. Ogbonnaya Onu ya bada sanarwar cewa zai shiga zaben fitar da gwani a zabe mai zuwa.

Ogbonnaya Onu ya roki APC ta tsaida shi a matsayin 'dan takara, domin a cewarsa yana da ilmin da zai shugabanci Najeriya, kuma shi mutum ne mai tausayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel