Masu harin Shugaban kasa sun karu, Minista na 4 a Gwamnatin Buhari ya shiga takara

Masu harin Shugaban kasa sun karu, Minista na 4 a Gwamnatin Buhari ya shiga takara

  • Ministan kimiyya da fasaha ya shiga sahun masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Yau Dr. Ogbonnaya Onu ya bada sanarwar cewa zai shiga zaben fitar da gwani a zabe mai zuwa
  • Ogbonnaya Onu ya roki APC ta tsaida shi domin a cewarsa yana da ilmin da zai shugabanci Najeriya

Abuja - Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Ogbonnaya Onu, ya ayyana burinsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

The Cable ta ce Dr. Ogbonnaya Onu ya sanar da Duniya wannan a wajen wani taro da ya kira a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu, 2022 a birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya bayyana kan shi a matsayin mutum mai matukar tausayi. Onu ya ce a lokacin da yake gwamna, a kyauta ake zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Onu ya ce ya kawo tsarin ganin likita kyauta ne saboda yadda ya ba mace muhimmanci. ‘Dan siyasar ya ce bai dace wata mace ta mutu wajen haihuwa ba.

Baya ga bangaren kiwon lafiya, Ministan ya ce jihar Abia ta gamu da cigaba a kowane bangare sa’ilin da ya yi mulki, don haka yake son shugabancin kasa.

“Ina so duka ‘yan Najeriya, musamman matasa su san cewa Najeriya za tayi kyau nan gaba. Ka da wani abu ya sa mutanen Najeriya su cire rai da makomarsu.”
“Ubangiji Madaukaki da ya halicce mu, ya bamu kasar da mu ke kauna, da duk abin da ake bukata domin ta zama jagora a fadin Duniya.” – Ogbonnaya Onu.
Ministan kimiyya
Dr. Ogbonnaya Onu Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda Onu zai gyara Najeriya

Idan Ogbonnaya Onu ya karbi mulkin Najeriya a 2023, ya ce zai yi amfani da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na zamani domin habaka tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Dr. Onu ya ce babu wata kasa a yau ko a jiya da ta cigaba, ba tare da ilmin kimiyya da fasaha ba.

“Na gamsu cewa ina da ilmi, sanin aiki, nagarta domin na yi karatu a daya daga cikin mafi kyawun jami’o’i a Duniya.”
“Ina da dattaku, sanin ya kamata, da hangen nesa na duk wani wanda za a yarda da shi, a zaba a matsayin shugaba.”

- Ogbonnaya Onu.

A karshe ya ce yana mai kira ga jam’iyyarmu ta APC, ta tsaida shi a matsayin ‘dan takararta na shugaban kasa domin mutane su zabe ni a matsayin shugaba.

Jaridar Vanguard ta rahoto Onu yana cewa idan ya karbi mulki, zai zama shugaban mai bautawa kasa.

Godswill Akpabio yana neman tuta

A baya kun samu labari cewa Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio zai shaidawa Duniya nufinsa na zama shugaban Najeiya a 2023 ba da dadewa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati ya hango matsala, yace da yiwuwar a fasa zaben Shugaban kasa

Idan da abubuwa sun tafi daidai, da tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya saye fam a ranar Larabar nan.Akpabio zai nemi takara ne a karkashin APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel