Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai

  • Tinubu, Osinbajo, sauran masu takaran kujeran shugaban kasa daga yankin Yoruba sun taru don sulhu
  • Dattawan yankin kudu maso yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda zasu hada kan yan takara daga yankin
  • Gwamnoni, jiga-jigan jam'iyyar APC, Ministoci, tsaffin gwamnoni, dss na hallare a zaman

Legas - Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido hudu da maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.

Manyan jigogin APCn biyu sun hadu ne a taron zaman hadin kai tsakanin yan takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC daga yankin kabilar Yoruba.

Dattawan yankin kudu maso yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za'a hada kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Dattawan sun hada da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba.

Wadanda ke hallare a zaman sun hada da Jigon APC Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi, da Ministar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola

Sauran sune Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu, Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, da gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola.

Hakazalika kawai ministan ayyuka da gidaje, Babajide Raji Fashola; Sanata Ibikunle Amosun; Sakataren APC Iyiola Omisore, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun, dss.

Kalli hotunan:

Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai
Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai
Asali: Facebook

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai
Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai Hoto: TSG

Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa

Kara karanta wannan

Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari dake neman takara sun yi murabus

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ba ɗan sa bane ba.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan gana wa da gwamnonin APC 12, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023.

Da aka tambaye shi me zai ce game da bayyana wa Duniya shiga takarar kujera lamba ɗaya da Osinbajo ya yi, wanda mutane da dama ke kallonsa a matsayin ɗansa a siyasance, Tinubu ya ce:

Asali: Legit.ng

Online view pixel