Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari 6 dake neman takara sun yi murabus

Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari 6 dake neman takara sun yi murabus

 • A ranar karshe na wa'adin da Buhari ya bada, sauran ministocin da sukayi jinkiri sun yi murabus
 • Mutum goma cikin Ministocin Buhari na son takara kujerun mulki a zaben 2023 da za'ayi a Febrairu
 • Mutum shida ciki na neman gadon kujerar Shugaban kasa yayinda biyu ke son zama gwamna

Abuja - Sauran Ministocin shugaba Muhammadu Buhari cikin goman da suka bayyana niyyar takara a zaben 2023 sun gabatar da takardun murabus dinsu.

Wannan ya biyo bayan zaman bankwanan da yayi da ministocin ranar Juma'a a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.

Shugaba Buhari a ranar Laraba, ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Yayinda shida (6) suke son zama shugabannin kasa, biyu (2) na son zama gwamnonin jihohinsu kuma biyu (2) na son zama Sanata.

Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari dake neman takara sun yi murabus
Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari dake neman takara sun yi murabus Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin Ministocin da sukayi murabus:

 1. Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi (Mai neman kujeran shugaban kasa)
 2. Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio; (Mai neman kujeran shugaban kasa)
 3. Minister kwadago, Chris Ngige; (Mai neman kujeran shugaban kasa)
 4. Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu (Mai neman kujeran shugaban kasa)
 5. Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba(Mai neman kujeran shugaban kasa)
 6. Karamin Ministan Man fetur, Timipre Sylva(Mai neman kujeran shugaban kasa)
 7. Karamin Ministan Ma'adinai da karafuna, Uche Ogar (Mai neman kujeran gwamnan jihar Abia)
 8. Ministar harkokin mata, Pauline Tallen (Mai neman kujeran Sanata)
 9. Ministan Shari'a, AGF Abubakar Malami (Mai neman kujeran gwamnan jihar Kebbi)
 10. Karamin ministan Neja Delta, Tayo Alasoadura (Mai neman kujeran Sanata)

Kara karanta wannan

2023: Jerin ministocin da suka yi murabus bayan umurnin Shugaba Buhari

Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, mutumin fako da yayi murabus

Karamin Ministan Ilmi Emeka Nwajuiba ne mutumin farko da yabi umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Emeka Nwajuiba ya yi murabus daga kujerarsa ta Minista ne domin maida hankali kan yakin neman zaben zama shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya bayyana hakan a zaman majalisar zartaswar ya gudana ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel