Da Dumi-Dumi: Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa

Da Dumi-Dumi: Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, da ɗansa bane
  • Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnonin APC, Tinubu yace ɗan sa be girma haka ba
  • Hakan na zuwa ne bayan Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana nufin gaje shugaba Buhari a 2023 dake tafe

Abuja - Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ba ɗan sa bane ba.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan gana wa da gwamnonin APC 12, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani da Hotuna: Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC jim kaɗan bayan Osinbajo ya shiga takarar 2023

Maataimakin.shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, da Bola Tinubu.
Da Dumi-Dumi: Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da aka tambaye shi me zai ce game da bayyana wa Duniya shiga takarar kujera lamba ɗaya da Osinbajo ya yi, wanda mutane da dama ke kallonsa a matsayin ɗansa a siyasance, Tinubu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba ni da wani ɗa da ya girma har ya iya ayyana abu mai girma kamar wannan. Muna da mutane a cikin jam'iyya ma su muradin jan ragama zuwa Ofishi mafi ƙoli a zaɓen ƙasar nan."

Me suka tattauna a ganawarsa da gwamnonin APC?

Haka nan kuma ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa kuma tsohon gwamnan Legas ya yi ɗan tsokaci kan abin da suka maida hankali yayin ganawa da gwamnonin APC.

Ya ce ya tattauna da gwamnonin jihohin da APC ke mulki ne domin neman haɗin kai, goyon baya da kuma kwarin guiwa daga gare su game da burinsa na ɗarewa kujerar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

Punch ta rahoto ya ƙara da cewa:

"Manufa ta anan ita ce na nemi haɗin kai, goyon baya da kwarin guiwar APC game da burina na zama shugaban ƙasa, wanda zai maye gurbin Muhammadu Buhari idan wa'adinsa ya ƙare."

A yau Litinin 11 ga watan Afrilu, mataimakin shugaban ƙasa ya amsa kiran wasu yan Najeriya, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

A wani bidiyo da ya watsa a kafafen sada zumunta, Osinbajo, ya ɗauki alƙawarin dasawa daga inda Buhari ya tsaya, tare da kammala ayyukan da ya fara.

A wani labarin kuma mun tattaro muku Tinubu, Osinbajo da sauran jiga-jigan APC da suka ayyana nufin gaje shugaba Buhari

A ranar Litinin 11 ga watan Afrilu, 2022, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya shiga tseren gaje Buhari a hukumance.

Kafin samun tutar takara karkashin APC, Osinbajo zai fafata da Tinubu, Amaechi da wasu mutum 4 da suka ayyana shiga takara.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Amaechi da wasu jiga-jigan APC 4 da Osinbajo zai gwabza da su ya gaji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel