2023: Gwamnan CBN, Emefiele, Shima Ya Biya N100m Kuɗin Fom, Ya Shiga Jerin Masu Son Gadon Kujerar Buhari

2023: Gwamnan CBN, Emefiele, Shima Ya Biya N100m Kuɗin Fom, Ya Shiga Jerin Masu Son Gadon Kujerar Buhari

  • Godwin Emefiele, gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, ya siya fom din takarar kujerar shugaban kasa a APC kan N100m
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu na kusa da Emefiele ne suka tafi ofishin APC da ke Abuja a yau Juma'a da safe suka karbo masa fom din
  • Hakan dai ya kawo karshen hasashen da aka dade ana yi kan yiwuwar takarar ta Emefiele ko kuma ba zai yi ba

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya siya fom din takarar shugaban kasa domin neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC, rahoton The Punch.

Daily Trust ta rahoto cewa Emefiele ya siya fom din takarar ta N100m a daga hannun sakataren tsare-tsare na jam'iyyar a International Conference Centre (ICC), Abuja, a safiyar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

2023: Gwamnan CBN, Emefiele, Shima Ya Biya N100m Kuɗin Fom, Ya Shiga Jerin Masu Son Gadon Kujerar Buhari
2023: Gwamnan CBN, Emefiele, Shima Ya Shiga Jerin Masu Son Gadon Kujerar Buhari. Hoto @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

Hakan ya kawo karshen hasashen da aka dade ana yi na cewa yana sha'awar gadon kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Wasu mukarraban Emefiele ne suka karbo masa fom din takarar

A rahoton da ta wallafa kan batun, Vanguard ta ce wasu na kusa da gwamnan na CBN ne suka tafi suka karbo masa fom din takarar shugaban kasar na APC.

An karbi fom din a madadin gwamnan na CBN misalin karfe 11.15 na safiyar yau Juma'a a cewar jaridar.

A watan Fabrairu 2014 ne tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Emefiele gwamnan CBN bayan ya sanar da dakatar da magabacinsa, Sanusi Lamido.

A shekarar 2019, tsohon shugaban na direktocin Zenith Bank ya kafa tarihi a matsayin mutum na farko da aka sabunta nadinsa a matsayin gwamnan na CBN.

Kara karanta wannan

Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

2023: Tinubu Ya Yi Magana Kan Ƙaruwar Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a APC

A bangare guda, jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce karuwar mutane da ke aiki don samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar alheri ne ga demokradiyya, The Guardian ta rahoto.

A kalla gwamnonin APC guda biyar, ministoci hudu da sanatoci da dama da wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar mai mulki ne suka fito neman takarar shugaban kasar.

Da ya ke magana bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, Tinubu ya ce fitowar yan takarar ya nuna shugabanni ba su yi watsi da Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164