2023: Tinubu Ya Yi Magana Kan Ƙaruwar Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a APC

2023: Tinubu Ya Yi Magana Kan Ƙaruwar Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a APC

  • Asiwaju Bola Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa ya yi magana game da karuwar yan takarar shugaban kasa a APC
  • Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ce karuwar yan takarar shugaban kasar alheri ne domin hakan na nufin shugabanni ba su yi watsi da Najeriya ba
  • Tinubu ya yi wannan jawabin ne yayin amsa tambayan manema labarai bayan ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyarar Sallah

Abuja - Jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce karuwar mutane da ke aiki don samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar alheri ne ga demokradiyya, The Guardian ta rahoto.

A kalla gwamnonin APC guda biyar, ministoci hudu da sanatoci da dama da wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar mai mulki ne suka fito neman takarar shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Tinubu: Ƙaruwar Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa Alheri Ne Ga Demokraɗiyya
'Karuwar Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa Alheri Ne Ga Demokraɗiyya, In Ji Tinubu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke magana bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, Tinubu ya ce fitowar yan takarar ya nuna shugabanni ba su yi watsi da Najeriya ba.

Daily Trust ta tattaro cewa tsohon gwamnan Jihar na Legas ya gana da Shugaban kasar ne a gidansa domin yi masa gaisuwar sallah.

"Karin yawan alheri ne. Yawansu na karuwa, kallubalen na karuwa hakan zai sa ka zurfafa tunaninka ka shirya yi wa Najeriya aiki. Duk saboda yi wa kasa hidima ne. Ka yi tunani sosai don kawo cigaba da bunkasa a rayuwar yan Najeriya.
"Alheri ne ga demokradiyya yadda mu da yawa ke fitowa takara, ba za mu yi watsi da kasarmu ba. Amma dai kujerar daya ne kuma mutum daya zai zama shugaba. Za mu yi hakan," in ji shi.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Yan APC za su hada kansu bayan zaben fidda gwani, in ji Tinubu

Jagaban na Borgu yayin amsa wata tambayar game da fargabar rabuwar kai a jam'iyyar ya ce yan jam'iyyar na APC za su hada kai wuri guda bayan zaben cikin gida.

Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna cewa yana goyon bayan demokradiyya ba tare da kumbiya-kumbiya ba.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164