Da duminsa: Gwamna Zulum ya sallami dukkan kwamishinonin jiharsa

Da duminsa: Gwamna Zulum ya sallami dukkan kwamishinonin jiharsa

  • Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sallami dukkan mambobin majalisar zartarwarsa
  • A takardar da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa hakan zai bai wa masu sha'awar neman kujerun siyasa nema kai tsaye
  • Zulum ya umarci dukkan kwamishinonin da su mika lamurran ma'aikatunsu ga manya sakatarorin ma'aikatun

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sauke dukkan kwamishinoninsa daga mukamansu.

Wannan lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2022 inda ya sanar da hakan a wata takarda da gwamnan ya fitar a shafinsa na Facebook da Twitter.

A cewar gwamnan, ya yi hakan ne domin bai wa duk masu burin tsayawa takarar wata kujerar siyasa fitowa su tsaya ba tare da sun karya doka ba

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Sallamar kwamishinonin wanda zai fara aiki a take, yana kunshe ne takardar da babban sakataren gudanarwa, Danjuma Ali, yasa hannu a madadin sakataren gwamnatin jihar.

An umarci dukkan kwamishinonin da su mika lamurran ma'aikatunsu hannun manyan sakatarorin ma'aikatun.

Zulum ya bayyana godiyarsa ga mambobin majalisar zartarwan kan gagarumar gudumawar da suka bada yayin da suke rike da ofisoshinsu kuma yayi musu fatan alheri a nan gaba.

Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.

Kara karanta wannan

Hadiza Sabuwa Balarabe, wasu mata 3 da ke rike da matsayin Mataimakin Gwamna a yau

Baya ga likitoci, ma'aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma'aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.

Kananan hukumomin: Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki cikin Bama wanda suke daga cikin wuraren da 'yan Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2014, ba tare da an zauna ba na kusan shekaru takwas har zuwa rufe sansanin 'yan gudun hijara da masu neman mafaka aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng