Wike: Ni Ne Kaɗai Ɗan Takarar Da Zai Iya Ƙwace Mulki Daga Hannun APC

Wike: Ni Ne Kaɗai Ɗan Takarar Da Zai Iya Ƙwace Mulki Daga Hannun APC

  • Gwamnan Jihar Ribas kuma dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Nyesom Wike ya ce shi kadai ne zai iya cin galaba akan APC
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Lokoja yayin jawabi ga wakilan PDP inda ya ce APC ta yi huji mai zurfi a kasar nan wanda sai dan siyasa mai karfi ne zai iya cikasa gurbin
  • Kamar yadda ya ce, kasar nan ta fuskanci rabe-rabe sakamakon rashin tsaro har a jihar shugaban kasa, don haka shi kadai ne ya ke da damar da zai iya ceto Najeriya

Jihar Kogi - Nyesom Wike, gwamnan Jihar Ribas sannan dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya ce shi ne kadai ne zai iya kai APC kasa, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana haka ne a Lokoja yayin jawabi ga wakilan jam’iyyar inda Wike ya ce APC ta haka rami mai zurfi a kasar nan don haka samun shugaban kasa mai halaye masu kyau da kuma karfi a siyasa ne kadai zai fitar da kasar daga cikin ramin.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Wike: Ni Ne Kaɗai Ɗan Takarar Da Zai Iya Ƙwace Mulki Daga Hannun APC
Ni Ne Kaɗai Ɗan Takarar Da Zai Iya Ƙwace Mulki Daga Hannun APC, In Ji Wike. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Ya ce kowa ya mayar da hankali akan wannan zaben mai zuwa

Kamar yadda The Punch ta nuna, Wike ya ce:

“Wannan kasar ba ta taba fuskantar matsalolin tsaro masu yawa ba kamar yanzu, har ta kai ga garin su shugaban kasa ma ba a bar shi a baya ba. Don haka Najeriya tana neman wanda zai ceto ta.
“Wannan zaben shi ne ko wanne dan Najeriya ya dace ya mayar da hankali akan shi. Wajibi ne mu hada kai don babu wanda zai iya yi shi daya; shugaban kasar da zai amshi mulki ne zai dage wurin amfani da abubuwan da ke hannu don kawo gyara a kasa.”

Ya ce jam’iyyarsa ta yi matukar masa kokari hakan ya sa zai tallafa wa ‘yan jam’iyyar ta hanyar samar da shugabanci na kwarai idan aka ba shi dama.

Kara karanta wannan

Akpabio: 'Gaskiyar' Buhari Ta Sa Na Shiga Jam'iyyar APC

Ya ce ko ba a tsayar da shi ba zai dage har sai an kwace mulki a hannun APC

A cewarsa:

“PDP ta yi min abubuwa da dama; ko da ban samu tikitin tsayawa ba, zan kasance a cikin jam’iyyar don mu amshe mulki daga hannun APC.
“Mu na bukatar shugaba mai kwarin gwiwa wanda zai iya daukar matakai inda ya dace. Mu na bukatar shugaban da ya san me ya dace kuma ya ke da damar tsayawa akan shi.
“Ku zabi wanda ku ke ganin ya na da karfin yi muku aiki. Ku zabe ni ku yi bacci. Zan yi muku aiki tukuru.”

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shigar Jonathan APC Zai Zama Ɗaya Cikin Abubuwa Mafi Ban Mamaki a Wannan Ƙarnin, In Ji Umahi

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel