Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza

Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza

- Hukuma DSS ta cafke hadimin gwamna Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai

- Hakan ya faru ne bayan ya caccaki Buhari tare da bukatar yayi murabus

- Dawisu ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza kuma wannan abun kunya

Hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS) ta damke Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun gwamna Kano, Abdullahi Umar ganduje bayan ya ce gwamnatin APC ta gaza.

A ranar Juma'a, Tanko-Yakasai ya bayyana damuwarsa a kan labarin kwashe yara mata na makarantar sakandaren kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara.

Bayan sa'o'i kadan da yin tsokacin a shafinsa a Twitter, an nemi Yakasai ko kasa ko sama an rasa, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani tsohon gwamna

Satar 'yan makaranta: DSS sun cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza
Satar 'yan makaranta: DSS sun cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza. Hoto daga @dawisu
Asali: Twitter

Amma a wata wallafa da shafin Twitter na jihar Kano yayi, an sanar da cewa Tanko-Yakasai na tare da jami'an tsaron farin kaya.

"Godiya ta tabbata ga Allah. Yanzu nan muka tabbatar da cewa Dawisu yana ofishin jami'an tsaro na fararen kaya," wallafar tace.

An yi yunkurin jin ta bakin Yakasai, amma wayoyinsa duk an kashe suke.

Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar DSS har yanzu bai yi tsokaci a kan lamarin ba.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

A wani labari na daban, hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta'addanci ko kuma tayi murabus.

A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar 'yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen 'yan ta'adda ko tayi murabus.

A yau Juma'a, 26 ga watan Fabrairu ne arewacin Najeriya ta tashi da mugun labarin sake kwashe wasu 'yan mata a makarantar kwana da ke Jangebe ta jihar Zamfara.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng