Rashin gaskiya: Matsala ta da Saraki, Tambuwal da 'yan takaran Arewa - Gwamna Wike
- Gwamna Wike ya bayyana cewa Bukola Saraki, Aminu Tmabuwal da masu neman shugabancin kasar na PDP daga arewa sun saba yarjejeniyar da aka cimma
- Wike ya bayyana cewa wannan shine makasudin matsalar da yake da ita da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawar kasar
- A cewarsa, Gwamna Samuel na jihar Benue ne kadai ya nuna goyon baya ga kudirinsa na son ya gaji Buhari a 2023
Abuja - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Litinin, ya bayyana matsalarsa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal kan batun mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu gabannin zaben 2023.
Wike ya ce ya sha goyon bayan yan takarar shugaban kasa daga arewa, inda yake mamakin dalilin da yasa wadanda ya marawa baya a zaben 2019 suke kara neman takarar shugaban kasa a 2023.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a sharin Politics Today na gidan talbijin din Channels.
Wike ya yi ikirarin cewa ya marawa Tambuwal baya wajen zama kakakin majalisar wakilai sannan ya marawa Saraki baya ya zama shugaban majalisar dattawa ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ne kadai ya nuna goyon bayansa ga takarar shugabancinsa, rahoton Punch.
Da aka tambaye shi game da alakarsa da Saraki, Tambuwal da sauran gwamnonin PDP, Wike ya bayyana cewa matsalar shi da yan Najeriya shine cewa “mutane basa son fadin gaskiya kuma bana jin dadi.”
Ya ce:
“Babu wani dan arewa da ke neman takarar shugaban kasa a yau da bana hulda da shi ko ban marawa baya ba. Su tara ne wadanda basu zo gareni don cewa ‘Wike, da kai ina ganin zan samu hanyata.’ Kuma na kan fada masu, ‘Na yarda, amma menene a kasa, me aka tanada?’
“Idan ka tambayi yawancin abokaina, matsalar da nake da shi da su shine cewa idan muka amince da wani abu, toh mu tsaya a kan haka. Idan har akwai wani dalili da zai hana hakan yiwuwa, toh a sanar da ni.
“Zan fada maku daya. Abun bakin ciki, yana tare da wani hazikin matashi wanda yan Najeriya ke sauraro – Bukola Saraki da girmamawa. Ina daya daga cikin wadanda suka tabbatar da ganin cewa ya zama shugaban majalisar dattawa. Yana a APC. Na yi rubutu a Twitter sannan na magantu kan hazikancinsa. Imma ka tsane shi ko n=baka son shi, wannan matashi na da hikima. Me zai sa ba zaka bari irin wannan mutumin ya jagoranci harkoki ba? Ban taba boye yadda nake ji a zuciyata ba.
“Dan uwana kuma abokina, Tambuwal, lokacin da yake son zama kakakin majalisa, gwamnati da PDP basu so ya zama kakakin majalisar ba. Ina daya daga cikin wadanda suka ce a’a, kada mu aikata haka. Na fito nace ya zama kakakin majalisar wakilan. Ko da ya so zama shugaban kasa, ina daya daga cikin wadanda suka ce shi matashi ne mai kwarewa kuma hakan ba wani abu bane. Cewa kada mu bi shekaru. Mutane na ta fada da ni…a kudu, a yamma, a arewa, a gabas. Duk sun yake ni. Me yasa kake kawo Tambuwa? Na ce ba zancen ina kawo Tambuwal bane. Nace na samu wanda nake zaton yana da duk abun bukata domin shugabanci.”
Wike ya bayyana cewa babu wanda zai ba hakurin don ya goyi bayan Tambuwal da Saraki a baya.
Gwamnan ya kara da cewar bai goyi bayan kudirin takarar shugaban kasa na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ba. Duk da haka, lokacin da Tambuwal ya sha kaye a hannun Abubakar a zaben fidda gwani, ya mika dukkan goyon bayansa ga tsohon mataimakin shugaban kasar.
Wike ya ce:
“Ina son kalubalantar kowa, kowani gwamna, kowani mutum a wannan jam’iyyar da za su ce sun ba Atiku goyon bayan da na bashi. A zahirin gaskiya, zan iya fada maku cewa a kudu maso kudu, a jihata ce kadai APC ta samu kaso 25 cikin 100 na kuri’u. atiku ya san cewa na fito gaba daya sannan na mara masa baya.”
A cewar Wike, akwai yarjejeniyar dattako cewa mulki ya ci gaba da kasancewa a arewa yayin da za a mika shi ga kudu a 2023.
Zaben 2023: Jerin ministocin Buhari da suka ki ajiye aiki bayan ayyana tsayawa takara
A wani labarin kuma, mun ji cewa duk da umurnin da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya baiwa masu rike da mukaman siyasa da ke neman takarar kujeru na su yi murabus wata guda kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wasu ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke hararar kujerun shugabanci a 2023 basu aikata hakan ba har yanzu.
Rashin ajiye aikin nasu ya kuma sabama sashi na 84(12) na dokar zabe, wacce ta nemi a ajiye aiki kafin shiga zaben fidda gwani.
Asali: Legit.ng