2023: PDP da APC sun gagari matasa, SDP ta shirya ba matasan Najeriya dama

2023: PDP da APC sun gagari matasa, SDP ta shirya ba matasan Najeriya dama

  • Jam'iyyar SDP ta samu karuwa yayin da wasu matasa suka hade da ita gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa
  • SDP ta alkawarta ba matasa tikitin tsayawa takara a mukamai matukar suka yi dandazo zuwa cikinta a yanzu
  • Wannan kira na SDP dai na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun APC da PDP ke kai ruwa rana kan batun tikiti

Abuja - Jam’iyyar SDP mai alamar doki ta bukaci kungiyoyin da matasa ke jagoranta a fadin kasar nan da su hada kai kana su shigo jam'iyyar baki dayansu.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Shehu Gaban ne ya bayyana hakan a yayin wata hadaka da jam’iyyar dimokuradiyyar matasa a Najeriya ta YDPN a Abuja, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Jam'iyyar SDP za ta ba matasa tikiti kai tsaye a zaben 2023
Tikiti kai tsaye: Yayin da ake kai ruwa kan tikitin takara a APC da PDP, matasa sun samu gata a SDP | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce SDP za ta ba duk wanda ke da sha'awar tsayawa takara tikiti kai tsaye idan ya amince ya dawo jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Shugaban YDPN, Zekeri Hashim, ya ce hadewarsu da SDP ya zama dole domin matasan Najeriya na bukatar hanyar da za su shiga harkokin siyasa cikin sauki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su waye matasan YDPN?

YDPN dai wata tawagar matasa ne da a shekarar 2020 ke bayan ballewar zanga-zangar EndSARS da aka yi a jihar Legas.

An kafa kungiyar ne da nufin yi mata rajista a matsayin jam'iyyar siyasa, amma hakan ya ci tura kasancewar hukumar zabe ta INEC ta ki amincewa da hakan.

Kin amincewar INEC na daga cikin dalilan da suka jawo tawagar ta hade da SDP domin cimma manufarta, kamar yadda shugabanta ya fada a wani rahoton Daily Sun.

2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

A wani rahoton mu na baya, kunji cewa, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya karbi fom din N100m na jam’iyyar APC domin tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Vanguard ta ruwaito cewa, jiga-jigan kungiyar goyon bayan Tiubu ta TSG ce ta dura cibiyar taron kasa da kasa ICC domin sayen fom din a madadin Tinubu.

An tattaro cewa Tinubu, wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel