2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, wasu jiga-jigan APC sun dura cibiyar taron ICC domin sayen fom din takara ga Tinubu
  • Tinubu dai na can kasar Saudiyya domin aikin Umrah, wanda ya samu wakilcin wasu manhyan 'yan siyasar kasar nan
  • Sayen fom din na zuwa ne gabanin zaben fidda gwani da jam'iyyar ta bayyana yi a nan gaba kadan kafin zaben 2023

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya karbi fom din N100m na jam’iyyar APC domin tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa, jiga-jigan kungiyar goyon bayan Tiubu ta TSG ce ta dura cibiyar taron kasa da kasa ICC domin sayen fom din a madadin Tinubu.

An tattaro cewa Tinubu, wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruwan sama, ana tantance Atiku, Saraki da sauran yan takara a PDP

Fom din takara ya shiga hannun Tinubu
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya karbi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC | Hoto: punch.ng
Asali: UGC

Hakazalika da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Agege a zauren majalisa, Babatunde Adejare; da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Faleke da Lawal da sauran masu biyayya ga jigo a siyasar jihar Legas ne suka karba masa fom din takarar shugaban kasa a hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2, Abuja, da misalin karfe 3 na rana.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Kara karanta wannan

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel