Bayan ya gana da Buhari, ‘Dan takara ya fadi matsayarsa a kan tsaida Jonathan a 2023

Bayan ya gana da Buhari, ‘Dan takara ya fadi matsayarsa a kan tsaida Jonathan a 2023

  • Gwamna Ben Ayade ya yi magana a game da shirin takarar Goodluck Jonathan a jam’iyyar APC
  • Farfesa Ben Ayade ya ce ba zai kalubalanci Jonathan idan ya zama wanda APC ta tsaida a 2023 ba
  • Ayade bai je Aso Villa da niyyar takara ba, amma shugaban kasa ya umarce sa da ya jarraba sa’arsa

Abuja - Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya ce zai yi aiki tare da Goodluck Jonathan idan har jam’iyyarsa ta APC ta tsaida shi takara a 2023.

Daily Trust ta rahoto Mai girma Farfesa Ben Ayade yana wannan magana bayan ya yi zama da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa.

Hakan na zuwa ne bayan rade-radin da ake ji cewa APC za ta ba Goodluck Jonathan wanda ya yi shekaru 5 yana mulki a PDP, takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Mai ba Buhari shawara ya lale Naira miliyan 50, ya saye fam din Gwamna a tashin farko

Da yake zantawa da ‘yan jarida a fadar shugaban Najeriya, Gwamna Ayade yace zai yi wa jam’iyya biyayya ko bai samu yadda yake so a zaben 2023 ba.

Buhari-Ayade
Gwamna Ayade tare da Shugaban kasa Hoto: Bashir Ahmaad
Asali: Facebook

Abin da Ayade ya fada a Aso Villa

“Ina matukar girmama shugaba Jonathan, saboda haka ba zan kalubalance shi ba. Na yi imani shugabannin jam’iyya za su yi abin da ya kamata,”
“Za mu dauki mataki a kan ‘dan takarar da zai kai jam’iyyarmu ga nasara a filin zabe.”
“Idan kun saurare ni da kyau, ina cikin masu matukar biyayya ga shugaban kasa, ina so in nemi takarar kujerar shugaban kasa, kuma zan shiga takara.”
“Amma duk lokacin da shugabannin jam’iyyata, watau APC su ka ji cewa shugaba Jonathan ne ‘dan takarar da ya fi cancanta, to zan goya masa baya.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Ba zan yi fada da masu gari ba – Ayade

“Ba zan taba yin fada da manya, masu rike da kasa, da shugabanni da Ubangiji ya damkawa madafan iko ba. Ban taba yin siyasar gaba da fada ba.”
“Idan kun san yadda na zama gwamna, kun san na nuna zan goyi bayan duk wanda gwamna yake so, sai nayi sa’ar zama ‘dan takararsa.”

A cewar Ayade, ya zo wajen Muhammadu Buhari ne domin marawa ‘dan takararsa baya, sai ya ce shi ma ya shiga sahun masu neman shugaban kasar.

Takarar Ita Enang

Bayan ya yi shekaru yana tare da Muhammadu Buhari, an ji labari Ita Enang ya fara shirin barin fadar Shugaban kasa, ya koma siyasa da kyau a 2023.

Fitaccen ‘dan siyasar zai nemi kujerar Gwamna a jihar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa domin ya kifar da gwamnatin PDP a Uyo.

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel