2023: Hadimin Shugaban Kasa ya koma gida, zai shiga takarar ‘Dan Majalisa a Kano

2023: Hadimin Shugaban Kasa ya koma gida, zai shiga takarar ‘Dan Majalisa a Kano

  • Bashir Ahmaad ya tabbatar da shirin fitowa takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jihar Kano
  • Hadimin shugaban kasar yana so ya wakilci mutanen mazabar Gaya, Ajingi da Albasu a zaben 2023
  • Ahmaad ya zauna da shugabannin kananan hukumomi da jagororin jam’iyyar APC a mahaifarsa

Abuja - Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmaad ya na shirin takarar ‘dan majalisa a zaben 2023.

Malam Bashir Ahmaad ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a ranar Talata. Ahmaad zai nemi kujerar Gaya/Ajingi/Albasu a majalisar wakilan tarayya.

Da yake bayani a shafin na sa, hadimin shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya ziyarci mahaifarsa watau Gaya da ke wajen birnin Kano a cikin makon nan.

A wannan ziyara, ‘dan siyasar ya samu yin zama na musamman da shugabannin kananan hukumomi, jagororin jam’iyyar APC da dattawan yankin.

Kara karanta wannan

Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

Ahmaad ya shaida masu cewa yana da burin fitowa takarar ‘dan majalisarsu a zabe mai zuwa.

Bashir Ahmaad ya ga soyayya da kauna

Hadimin na Mai girma Muhammadu Buhari ya gode da abin da mutanen Gaya da Albasu suka yi masa, ya ce al’umma sun nuna masa kauna da soyayya.

Hadimin Shugaban Kasa
Bashir Ahmaad a Gaya Hoto: @bashahmad
Asali: UGC

Tun 2015 dai Bashir Ahmaad yake aiki a fadar shugaban kasa a matsayin mai ba Muhammadu Buhari shawara, an sake ba shi wannan mukami a 2019.

Kafin ya hadu da Muhammadu Buhari wanda shugaban kasa bayan zaben 2015, matashin ya yi aikin jarida a Rariya da jaridar nan ta Leadership Hausa.

Legit.ng Hausa ta na da labari Ahmaad ya tashi ne a garin Gaya da ke jihar Kano, har ya yi digiri a fannin aikin jarida a shahararriyar jami’ar nan ta Bayero.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Hadimin shugaban kasa ya shigo siyasa

Matashin ya nuna hotonsa tare da manyan gari, ya na mai nuna cewa zai dauki shawarar na gaba da shi tare da sauraron kukansu idan har ya cin ma burinsa.

A wani jawabi da ya yi, Ahmaad ya ce ba abinda ya fi dadi kamar ganin tsantsar soyayya daga jama’a, ya yi alkawarin zai wakilci al’ummarsa da gaskiya.

Martanin mutane a Facebook

Jama’a su na ta yi wa Bashir Ahmaad fatan alheri, su na yi masa addu’o’i a dandalin Facebook. Ga abin da wasu ke fada:

"Ina yi maka fatan ka wakilci mutanen ka idan an zabe ka. Ina taya ka murna Honarabul."

– Garba Ahmed

"Allah ya baka sa'a. Ina Maka fatan alkhairi, duk da cewa ni Dan jahar Borno ne, Amma gaskiya Ina fatan Allah yasa kasamu mukamin da kake muradi in shine Mafi alkhairi. All the best Mallam Bashir."

– Mukhtar Habib

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

"Allah ya bada nasara Honarabul."

– Mustafa T. Gabari

"Za ka yi nasara idan Allah ya yarda."

– Saifullahi Umar Naira

"Hakika mutanen Gaya Ajingi da kuma Albasu sun amsa kira malam Bashir Ahmad sai fatan Allah ya shiga cikin al'amarin."

– Balarabe Babale Gajida

Asali: Legit.ng

Online view pixel