Gwamna Umahi ya lale miliyan N100m ya karɓi Fam ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

Gwamna Umahi ya lale miliyan N100m ya karɓi Fam ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

  • Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya biya kuɗi naira miliyan N100m ya karɓi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC
  • Gwamnan jihar dake kudancin Najeriya ya kawo ƙarshen yaɗa rahoton cewa ya canza ra'ayi zuwa neman sanatan Ebonyi ta kudu
  • Umahi ya roki yan Najeriya su goya masa baya ya gaji Buhari, ya tabbatar musu ba zai ba su kunya ba

Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Talata, ya sayi Fom ɗin nuna sha'awar takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Umahi ya sanar da haka ne a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook da daren ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Hakan ya kawo karshen labaran da ake yaɗa wa a ciki da wajen jihar Ebonyi cewa gwamnan ya jingine neman takarar shugaban ƙasa, ya koma takarar Sanata mai wakiltar Ebonyi ta kudu.

Gwamna David Umahi na Ebonyi.
Gwamna Umahi ya lale miliyan N100m ya karɓi Fam ɗin takarar shugaban ƙasa a APC Hoto: Governor Umahi/facebook
Asali: Facebook

A makon da ya gabata, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ƙalubalanci Umahi da cewa ya fito su gwabza a takarar shugaban kasa idan ya cika cikakken mutum.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umahi ya biya Miliyan N100m

Da yake tabbatar da karɓan Fom, Gwamna Umahi ya nuna takardan shaidar biyan kuɗi N100,000,000 na Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC.

Gwamnan ya roki yan Najeriya su goya masa baya har ya ci nasarar zama shugaban ƙasa na gaba a 2023.

Ya ce:

"Yan Najeriya, ba zan baku kunya ba. Duk da kwan gaba kwan bayan tattalin arziki a Ebonyi, mun ci nasarar canza ta daga yanda take zuwa birnin Dubai na Najeriya."

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

"Zamu yi abinda ya zarce haka a matakin ƙasa, amma ba zamu cimma nasara ba dole sai da amincewar ku (yan Najeriya)."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa gwamna Umahi ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC ne a watan Nuwamba, 2020. A PDP ya ci nasarar lashe zaɓen gwamna har sau biyu.

A wani labarin kuma Sanata Stella Oduah ta fice daga jam'iyyar APC, ta koma tsagin hamayya PDP

Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa, Sanata Stella Oduah, ta tabbatar da sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.

Sanatar wacce tana ɗaya daga cikin masu kai kudiri, ta ɗauki wannan matakin ne bayan zaman shawari da jiga-jigan PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel