Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

  • Yahaya Bello a shirye yake da duk wani wanda yake neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Gwamna na jihar Kogi ya nuna bai jin shakkar gwabzawa da kowane mai neman shugabanci a 2023
  • Bello ya yi wannan magana ne a lokacin da ake rade-radin Goodluck Jonathan zai nemi tikitin APC

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa babu wani mai neman takarar kujerar shugaban kasa da yake shakka a jam’iyyarsu ta APC.

Jaridar Daily Trust ta ce Mai girma gwamnan ya bayyana wannan ne jim kadan bayan ya biya kudi, ya karbi fam din takarar shugaban APC a zaben 2023.

Da yake zantawa da manema labarai asakatariyar jam’iyyar APC da ke garin Abuja, gwamnan na Kogi ya ce bai tsoron kowa a zaben da za ayi a watan Mayu.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Bello bai kama sunan kowa ba, amma zancensa ya yi nuni ga Goodluck Jonathan wanda ya yi shekaru fiye da biyar yana mulkin Najeriya a jam'iyyar PDP.

Damukaradiyya kenan - Bello

“A tsarin damukaradiyya, kowa zai iya goyon bayan duk wanda yake so, amma ina tabbatar maku da cewa jam’iyyarmu ta na da tsare-tsare da dokokinta.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kuma na tabbatar cewa duk wadannan za su taimaka mani, kuma ko kadan ba na jin tsoron tarihin wani ko wanene shi.” - Yahaya Bello.
Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

Bello na tare da jama'a

“Ina da yakinin cewa ina tare da masu rinjaye, ina da mata da matasa, masu fama da nakasa duk su na tare da ni. Shugabanni da talakawa na baya na.”
“Sannan kuma abin da ya fi kowane muhimmanci, na rike Allah madaukakin Sarki.” - Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Bayan ya gana da Buhari, ‘Dan takara ya fadi matsayarsa a kan tsaida Jonathan a 2023

APC za ta samu kuri'u miliyan 21?

The Cable ta rahoto Gwamna Bello yana cewa akwai mutane miliyan 21 da suka shirya zabensa a matsayin shugaban kasa muddin jam’iyya APC ta ba shi tuta.

Bello ya ce idan shi ne ya yi takara a zaben 2023, idan aka dunkula sauran ‘yan takaran jam’iyyun adawa, duk ba za su samu rabin kuri’un da zai tashi da su ba.

Gwamnan ya ce abin da ke gabansa a yanzu shi ne shawo kan ‘yan jam’iyya da shugabannin APC da duk ‘yan Najeriya su mara masa baya domin a ba shi tikiti.

Wa’adin da aka ba Jonathan

A ranar Larabar nan aka ji wata kungiya mai suna Youths Network for Nigeria Union ta tursasa Goodluck Jonathan ya ayyana takara a APC bayan azumi.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Saiki, ya ce matasa 20, 000 za su yi dafifi a ofishin Dr. Jonathan, har sai ya yarda shiga APC domin ya nemi shugabancin kasar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel