Sanata Stella Oduah ta fice daga jam'iyyar APC, ta koma tsagin hamayya PDP

Sanata Stella Oduah ta fice daga jam'iyyar APC, ta koma tsagin hamayya PDP

  • Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa, Sanata Stella Oduah, ta tabbatar da sauya sheƙa daga APC zuwa PDP
  • Sanatar wacce tana ɗaya daga cikin masu kai kudiri, ta ɗauki wannan matakin ne bayan zaman shawari da jiga-jigan PDP
  • Misis Oduah, tsohuwar ministar Sufurin jiragen sama ta cimma nasarori da yawan gaske tun bayan zuwanta majalisa

Anambra - Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra da arewa a majalisar dattawa, Sanata Stella Oduah, ta sanar da sauya shekarta daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Sanata Stella ta kammala sauya shekarta ne ranar 28 ga watan Afrilu, 2022 bayan ta je tantancewa Sakatariyar PDP ta ƙasa dake Wadata Plaza, kamar yadda Vangaurd ta rahoto.

Sanata Stella Oduah.
Sanata Stella Oduah ta fice daga jam'iyyar APC, ta koma tsagin hamayya PDP Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Bayan kammala tantance ta da kuma ɗumbin nasarorin da ta samu na kawo cigaba da matsayin sanata, komawarta PDP ka iya ƙara wa jam'iyyar ƙarfi da nasara a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Sanata Oduah na ɗaya daga cikin wakilai nagari daga jihar Anambra kuma a ko da yaushe ana ganin ƙimarta a jam'iyyar PDP kafin ta fice a watan Agusta, 2021.

Meyasa ta sake komawa PDP?

Rahoto ya nuna cewa bayan zaman shawari da manyan jiga-jigan PDP da kuma duba ƙarfinta a siyasa da halin da ƙasa ke ciki, Sanatar mai farin jini ta koma jam'iyyar da ake ganin girmanta.

Ko a kwanan nan, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta gabatar da kudiri a gaban majalisar dattawa na gina babbar cibiyar duba lafiya ta ƙasa a Onitsha.

Haka nan tana daga cikin muryoyin da suka fi haƙiƙicewa kan buƙatar matasa su tashi tsaye su kware a fannoni da dama, ko dan Najeriya ta shiga zamani.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Dawafi na musamman da aka yi don Tinubu a Masallacin Harami, yace a yiwa Najeriya addu'a

Sanatar ta shiga gaba ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin yan mazaɓarta sun samu damarmakin aikin yi da kuma wakiltar jiharsu wakilci mai kyau.

Daga cikin abubuwan da ta yi akwai, gyara da sake gina hanyoyi, gina azuzuwa a makarantu, ICT, rijiyoyin burtsatse da sauran su.

A wani labarin kuma Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Wani makusancin Bankole ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya fara shirye-shirye, kuma zai karɓi Fom mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel