‘Dan takaran PDP ya kai karar Jam’iyya a kotu, ya bukaci a dakatar da zaben tsaida gwani

‘Dan takaran PDP ya kai karar Jam’iyya a kotu, ya bukaci a dakatar da zaben tsaida gwani

  • Cosmas Ndukwe ya hakikance a kan cewa lokacin Kudu maso gabas ne su shugabanci Najeriya
  • Babban jigon na PDP a jihar Abia ya kai karar jam’iyyarsa a kan wannan a wani kotu da ke Abuja
  • Lauyan da ya tsayawa Hon. Ndukwe ya na so a fasa zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa a PDP

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Abia, Cosmas Ndukwe, ya shigar da karar jam’iyyar PDP a babban kotun tarayya a Abuja.

The Cable ta ce Hon. Cosmas Ndukwe ya na so Alkali ya dakatar da jam’iyyar hamayyar ta PDP daga gudanar da zaben fito da ‘dan takarar shugaban kasa.

‘Dan siyasar ya shigar da karar ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu 2022. Yanzu haka maganar da ake yi saura kwanaki 30 rak su ka rage ayi wannan zabe.

Kara karanta wannan

2023: Jam’iyyar PDP ta na hannun Shugaban Jam’iyyar da Kwankwaso ya bari inji Kotu

Rahoton ya ce Ndukwe ya shigar da karar mail amba FHC/ABJ/CS/508/2022 a babban kotun da ke zama a garin Abuja ta hannun wani lauya, Paul Erokoro.

Barista Erokoro ya nemi kotu ta tsaida yin zaben fitar da ‘dan takarar saboda jam’iyyar PDP ta ki bada umarnin a fito da ‘dan takara daga kudu maso gabas.

Ndukwe wanda ya taba rike kujerar Kwamishina a gwamnatin Abia, yana ganin yankinsu na kudu maso gabas ya kamata a ba tikiti zaben shekarar badi.

‘Dan takaran PDP
Atiku Abubakar mai neman takara a PDP Hoto: @AAbubakar.org
Asali: Facebook

Kalu Agu Kalu zai kare PDP

Lauyan da ya tsayawa jam’iyyar PDP, Kalu Agu Kalu ya kulabalanci wannan roko, ya bukaci Alkali mai shari’a Donatus Okorowo ya yi watsi da karar a gabansa.

Bayan sauraron duka bangaren, gidan talabijin na Channels TV ya ce Donatus Okorowo ya daga shari’ar. Za a cigaba da sauraron karar a ranar 5 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

A mako mai zuwa, Okorowo zai saurari hujjojin lauyan PDP a kan abin da zai hana a fasa zaben.

A baya an ji cewa Cosmas Ndukwe ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a PDP. Kafin yau, ya rike shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Abia.

'Yan takara na ta yakin zabe

A yau aka ji Kungiyar Peter Obi Support Network ta na taya Peter Obi yakin zama shugaban kasa. A kan haka POSN ta sha alwashin tara gudumuwar akalla N6bn.

Ranar 28 ga watan Mayu aka tsaida a matsayin ranar da PDP za ta fitar da ‘dan takarar shugaban kasa. Duk wanda ya yi nasara zai rikewa jam’iyyar tuta a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel