Magoya baya za su tara Naira Biliyan 6 domin ‘Dan takararsu ya zama Shugaban kasa

Magoya baya za su tara Naira Biliyan 6 domin ‘Dan takararsu ya zama Shugaban kasa

  • Kungiyar nan ta Peter Obi Support Network ta na taya Peter Obi yakin zama shugaban kasar Najeriya
  • Peter Obi Support Network ta rantsar da shugabannin shiyyoyi da za su yi mata aiki a zaben 2023
  • POSN ta ce magoya miliyan shida da ake da su a Najeriya, kowa zai ba Obi gudumuwar akalla N1000

Abuja - Wata kungiyar magoya baya mai suna Peter Obi Support Network ta fara kokarin ganin tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya lashe zaben 2023.

Tribune ta ce wannan kungiya ta soma jawo hankalin mutanen Najeriya domin su marawa Peter Obi baya, ya zama shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar PDP.

‘Yan kungiyar Peter Obi Support Network za su nemi gudumuwar akalla N1000 daga wajen magoya baya miliyan shida da Obi ke da su a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Wannan kungiya ta ce idan aka tara wadannan kudi, ana sa ran samun Naira biliyan shida wanda za ayi amfani da su wajen yakin zama shugaban kasa.

An nada shugabannin shiyyoyin POSN

A ranar Litinin ne Peter Obi Support Network ta bayyana haka wajen kaddamar da shugabanninta na yankuna. An yi taron ne a babban birnin tarayya na Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban taron da aka yi a ranar, Sheikh Rufai Al-Siddiq ya ce kungiyar ta na da sama da mutane miliyan shida da suka yi rajista, kuma kowa zai biya N1000.

Peter Obi
Peter Obi a Bayelsa Hoto: @ubanijnr; Chidinma Ubani
Asali: Facebook

Sheikh Rufai Al-Siddiq ya ce akwai wadanda za su biya fiye da wannan kudin da aka kayyade.

POSN: Obi yana da jama'a, ya cancanta

Kamar yadda aka rahoto, Rufai Al-Siddiq ya ce gudumuwar da POSN za ta samu zai nuna yadda Peter Obi ya samu karbuwa, har a wajen Musulman kasar nan.

Kara karanta wannan

An ba Jonathan kwanaki 7 ya shiga APC, ya fito takarar Shugaban kasa da karfi-da yaji

“Ya kamata a ba ‘dan siyasa daga Kudu maso gabas dama. Hakan zai taimaka wajen samun hadin-kai da gyara alakar da ke tsakanin al’ummar Najeriya.”
“Peter Obi shi ne ya fi kowa cancanta ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.” - Rufai Al-Siddiq

Manufar kungiyarmu inji Ngogbehei

Jaridar Punch ta ce Darektan tsare-tsare na kungiyar ta POSN, Marcel Ngogbehei, ya samu yi wa mutane jawabi a wajen taron da aka shirya ta kafar yanar gizo.

Mista Ngogbehei ya ce burinsu shi ne samar da hadin-kai da zaman lafiya tsakanin ‘yan kasa. Sannan kuma kungiyarsu ta samu cewa wajen zaben shugabanni.

...Saraki ya na neman tikiti a PDP

Da ya ziyarci jihar Kuros Riba, an ji Abubakar Bukola Saraki ya bayyana irin 'dan siyasar da mutanen Najeriya ke bukata ya shiga fadar Aso Villa a zaben 2023

Tsohon Gwamnan ya yi alkawarin cewa idan ya zama Shugaban kasa, matasa za su rike kujerun Ministocin tarayya a gwamnatinsa, sannan jama’a za su samu aiki.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel