An ba Jonathan kwanaki 7 ya shiga APC, ya fito takarar Shugaban kasa da karfi-da yaji

An ba Jonathan kwanaki 7 ya shiga APC, ya fito takarar Shugaban kasa da karfi-da yaji

  • Youths Network for Nigeria Union ta bukaci Goodluck Jonathan ya shiga jam’iyyar APC mai mulki
  • Bayan haka wannan kungiya ta matasa ta ce tsohon shugaban kasar ya tsaya takara a zaben 2023
  • Shugaban YNNU ya ce matasa 20, 000 za su tare a ofishin Jonathan har sai ya yarda da bukatarsu

Abuja - Kungiyar Youths Network for Nigeria Union ta ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wa’adi ya karbi katin zama ‘dan jam’iyyar APC.

Jaridar Tribune ta ce kungiyar matasan na YNNU su na so Goodluck Jonathan ya yi rajista da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a mazabarsa a Otuoke.

Shugaban kungiyar ta YNNU na kasa, Ibrahim Saiki ya yi wannan kira yayin da ya shirya gangami na musamman a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Ibrahim Saiki yake cewa idan har tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi rajista da APC, hakan zai ba shi damar sayen fam din shiga takarar shugaban kasa.

Me zai faru bayan mako daya?

An rahoto shugaban kungiyar matasan yana cewa idan tsohon shugaban kasar ya watsa masu kasa a ido bayan kwanaki bakwai, to za su mamaye ofishinsa.

Saiki ya shaidawa manema labarai matasa za su dura ofishin Jonathan da ke Abuja, su tursasa shi sai ya shiga takara idan ya nemi ya ki yin abin da suke so.

Shugaba Jonathan
Jonathan a lokacin ya na Shugaban kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“An bukace mu da mu yi kira ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi maza ya karbi katin zama ‘dan APC a mazabarsa a Otuoke, jihar Bayelsa.”
“Ya yi wannan a cikin matukar girmamawa da karramawa kwanaki bakwai bayan azumin Ramadan.”

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

“Idan bayan kwanakin nan bakwai su ka wuce, Jonathan bai yanke shawara ba, za mu sake kai ziyara zuwa ofishinsa domin mu nemi mu yi zama na biyu.”
“Ya kamata a sani sama da mutum 20, 000 da ke cikin kungiyarmu mai dauke da mutane har 500, 000 a fadin kasar nan sun shirya tarewa a ofishin Jonathan.”
“Za mu cigaba da zama a ofishin na sa har tsawon lokacin da zai dauke shi ya yanke shawara.” - Ibrahim Saiki

Shirin dawo da Jonathan mulki

A makon nan ku ka ji cewa wasu Gwamnoni biyu da ake ji da su a APC ne suka shiga suka fita domin dawo da Goodluck Jonathan kan kujerar shugaban kasa.

Gwamnonin su na so Jonathan ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 ne saboda su samu kujerar mataimakin shugaban kasa a saukake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng