Yadda Gwamnoni 2 a Arewa ke kokarin dawo da Jonathan Aso Villa a jam’iyyar APC da wayau

Yadda Gwamnoni 2 a Arewa ke kokarin dawo da Jonathan Aso Villa a jam’iyyar APC da wayau

  • Gwamnoni biyu da ake ji da su a APC ne suka shiga suka fita domin dawo da Goodluck Jonathan
  • Wadannan Gwamnoni su na so Jonathan ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023
  • Hakan zai sa masu wannan buri su samu kujerar mataimakin shugaban kasa har su karbe mulki

Abuja - Wasu gwamnoni da ta ke da ta-cewa a Najeriya su na cikin wadanda ke faman kutun-kutun wajen ganin an dawo da Goodluck Jonathan kan mulki.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar 27 ga watan Afrilu 2022, ya bayyana cewa wadannan gwamnoni su biyu su na cikin na kusa da Muhammadu Buhari.

Maganar da ake yi, gwamnonin jihohin sun saidawa wani bangaren fadar shugaban kasa wannan ra’ayi na shigo da tsohon shugaban Najeriyar cikin zabe.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Majiyar ta shaidawa jaridar sunayen wadannan gwamnoni biyu, amma har yanzu abin yana a duhu domin sun yi tafiya zuwa kasar waje a yanzu balle a ji ta su.

Daya daga cikin gwamnonin ya fito ne daga yankin Arewa maso yamma (inda Muhammadu Buhari ya fito), dayan kuma daga bangaren Arewa maso gabas.

Asalin wannan tafiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar da ta wuce aka fara wannan shirye-shirye, daga baya gwamnonin suka yi watsi da maganar Jonathan, su ka fara kokarin kawo Godwin Emefiele.

Jonathan cikin Aso Villa
Jonathan da Buhari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ganin zai yi wahala takarar gwamnan CBN watau Emefiele ta kai labari, sai gwamnonin su ka sake dawowa kan maganar farko, na tsaida Jonathan a APC.

Yadda abin yake - Tsohon Gwamna

Wani tsohon gwamna wanda ya san abin da yake faruwa ya ce gwamnonin nan biyu da ake magana sun yi wa Dr. Jonathan tayin sake neman shugabanci.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

“Su na yin wannan ne domin su taka Asiwaju Tinubu bayan sun fahimci cewa mataimakin shugaban kasa ba zai iya ja da shi sosai a jam’iyya ba.” - Majiya.

Tsohon gwamnan ya ce masu wannan su na neman hanyar da za su karbe mulki ne a 2027, kuma za su iya tashi kujerar mataimakin shugaban kasa a shekarar badi.

Muhammadu Buhari ya gamsu?

“Babban mai goyon bayansa shi ne shugaban kasa. Ku na tunanin zai fara tun farko idan Baba bai tare da shi? Jawo shi suka yi domin sun fi gamsuwa ya yi mulki.”

Tsohon shugaban kasar bai yi watsi da wannan magana ba, za a iya cewa ya na nuna ya gamsu da shirin. A gefe guda Muhammadu Buhari bai ce komai ba.

A je a dawo game da takarar Jonathan

Kwanakin baya an ji labari bayan an yi ta dogon lissafi, an yi watsi da maganar shigo da Goodluck Jonathan cikin Jam’iyyar APC, har ta kai a ba shi takara a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Yanzu abubuwan su na canzawa, Jonathan ya kyankyasawa magoya bayansa cewa babu mamaki ya sake neman kujarar da ya yi shekaru kusan biyar a kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel