Bayan ya sa labule da Buhari: Ana rade-radin Tambuwal zai sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa gwamnan jihar Sokoto, Gwamna Aminu Tmabuwal na iya sauya sheka daga PDP zuwa APC
- An fara rade-radin ne bayan Tambuwal ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar villa yayin da shirin tsayar da dan takarar yarjejeniya a PDP ya rushe
- Sai dai kuma, hadimin gwamnan na jihar Sokoto ya yi watsi da lamarin, ya ce idan ma akwai wani shiri na yin hakan, lokaci zai bayyana
Abuja - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wata ganawar sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu.
Ganawar tasu na zuwa ne kasa da mako guda bayan shirin dattawan arewa na tsayar da dan takarar yarjejeniya a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya wargaje.
Sai dai kuma, wannan ganawa da Tambuwal ya bayyana a matsayin na sirri ya haifar da hasashe kan yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP a karo na biyu, jaridar Leadership ta rahoto.
Gwamnan wanda ya kasance daya daga cikin masu neman tikitin shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa baya cikin yan takarar yarjejeniya da kungiyar dattawan arewa karkashin Farfesa Ango Abdullahi suka tsayar.
Dattawan arewar dai sun nemi a tsayar da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ko tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
A lokacin da manema labaran fadar shugaban kasa suka tunkari gwamnan na jihar Sokoto bayan ganawar, ya ki cewa komai kan sakamakon ganawar tasa da shugaban kasar wanda ya kasance jigon APC, inda ya ce ziyarar da ya kai villa na sirri ne.
Tambuwal wanda ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin PDP yana da tarihi na sauya jam’iyyar siyasa.
A 2003, an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Kebbe/Tambuwal a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
Yan watanni kafin zaben 2007 sai ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Democratic People’s Party (DPP) tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa. Amma da DPP ta hana masa tikitin tazarce, sai Tambuwal ya koma ANPP inda ya yi nasarar samun tikitin zarcewa.
Sannan a lokacin da dan takarar gwamnan jihar Sokoto na ANPP, Alhaji Aliyu Wamakko ya koma PDP a 2007, sai Tambuwal ya sake binsa zuwa jam’iyyar.
A ranar 28 ga watan Oktoba, 2014, yayin da ake shirin zaben 2015, a matsayinsa na kakakin majalisar wakilai, Tambuwal ya bar PDP zuwa APC kuma ya yi nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Sokoto.
Ya kuma sake dawowa PDP a yayin da ake shirin zaben 2019 sannan yay i takarar neman tikitin shugaban kasa na jam’iyyar.
Hadimin Tambuwal ya yi martani a kan jita-jitar cewa zai sauya sheka daga PDP
Amma da yake martani a kan sakamakon ganawar tasa, hadimin Tambuwal, Mohammed Bello, ya yi watsi da rade-radin, yana mai cewa shugaban kasar ne ya gayyace shi wanda bai kamata a fassara shi da cewar yana son sauya sheka ba.
Gwamnan ya fada ma jaridar Leadership cewa ziyarar da gwamnan ya kai villa bai da nasaba da rushewar tsarin tsayar da dan takarar yarjejeniya a PDP.
Bello ya ce:
"Toh, lamarin shine cewa shi gwamna ne mai ci kuma idan shugaban kasa ya nemi ya zo ya gan shi, bai kamata a fassara hakan a matsayin yana son sauya sheka ba.
“Tsarin gwamnatin shugaban kasa tsari ne na jam’iyyu da yawa; duk wanda yake matsayin gwamna a kowane lokaci yana iya ganawa da abokan aikinsa da manyansa na kowace jam’iyya. To ni haka nake kallon abun. Ba na son in fassara taron a tsarin jam’iyya.”
Da aka tambaye shi game da zuwan ganawar yan kwanaki bayan rushewar tsarin yarjejeniya, Bello ya ce:
“Kamar yadda na fadi, tsarin yarjejeniyar bai cimma nasara ba. Amma shi dan siyasa ne kuma ya saba da juyawar abubuwa amma wannan baya nufin zai tsere haka kawai.
“Idan har za a samu irin wannan yunkuri a nan gaba kadan, ina ganin lokaci zai bayyana. Nawa lissafin shine, yaya zai kasance, shi dan takarar shugaban kasa ne a PDP sai kuma ya zo yana so ya bar PDP zuwa APC, kan wani dalili?
“Idan ya rasa kudirinsa a PDP, toh me APC za ta bashi. Ya san dalilin da yasa ya gana da shugaban kasa a kamara. Ni da ku hasashe kawai za mu iya yi kan haka.”
Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu
A wani labarin, mun ji cewa wata sabuwar doka da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka saki a ranar Talata, ta tanadi cewa ya zama dole duk masu mukaman siyasa da ke da niyan shiga zaben fidda gwaninta a dukkan matakai su yi murabus akalla kwanaki 30 kafin zaben.
Bisa ga sabuwar dokar, wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke neman takarar shugaban kasa kamar su ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da takwaransa na kwadago, Chris Ngige, suna da sauran kwanaki uku kacal su yi murabus ko su hakura da takararsu.
Hakan ya kasance ne duba ga cewa zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC, zai gudana a tsakanin ranar 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni kamar yadda yake a jadawalin jam’iyyar mai mulki.
Asali: Legit.ng